Daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun zargi wasu malamai da hada kai don kawo cikas a shari’ar da ake yi da malaminsu.
An tasa keyar Abduljabbar zuwa kotun Musulunci, daga bisani ya daukaka kara zuwa babbar kotu da ke jihar Kano.
Daliban da ke karkashin kungiyar Ashabul Kahfi Warrakeem ne suka bayyana haka ta bakin kakakinta, Ibrahim Abdullahi.
Wasu dalibai da magoya bayan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da aka kama saboda ya ci mutuncin Manzon Allah sun koka kan yadda wasu malamai suka hada kai don su kawo cikas a daukaka karar da ya shigar.
Sheikh Abduljabbar dai an tasa keyarsa zuwa kotun sharia’ar Musulunci da ke Kano bisa zargin zagi da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW), inda aka hukunta shi amma ya daukaka kara a babbar kotun jihar Kano.
Dalibai wadanda suke karkashin kungiyar Ashabul Kahfi Warrakeem ta Najeriya ta bakin kakakin kungiyar, Ibrahim Abdullahi Warure sun yi wannan zargin ne a ranar Lahadi 21 ga watan Mayu a Kano yayin wani taro.
An yanke hukuncin kisa ga Sheikh Abduljabbar Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022, kotun shari’a ta yanke hukuncin kisa ga malamin addinin, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Sanarwar tace: “Mun samu bayanai cewa malaman da suka hada kai akan zargin da ake yi wa malam na farko, yanzu ma sun fara barazana musamman ga gwamnatin da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu da nufin cewa babu wanda ya isa ya sa a sake malam.
“Mun yi Allah wadai da bata suna da suke wa Sheikh da kuma barazana wa kotun da ake sauraran karar.”
Ba su son zaman lafiya a Kano da ma Najeriya baki daya Sanarwar kamar yadda jaridar Daily Post ta tattaro, ta kara da cewa: “Wannan kulle-kulle ne don ganin sun kawo cikas ga zaman lafiyar wannan jiha da ma kasa baki daya, idan har Sheikh Abduljabbar ya yi nasara a kotun.
Warure ya bukaci jam’ian tsaro da sauran wadanda abin ya shafa da su ja kunnen wadannan malamai a kan batanci da bita da kulli da suke yi wa malamin nasu.
Hukuncin Abduljabbar : Maganganun Maqary, da sauran Malaman Musulunci
A wani labarin, Malaman Musulunci da dama sun yi maganganu da mai da martani akan hukuncin lkisa ga Abduljabbar Kabara.
Legit.ng Hausa ta tattaro abin da wasu daga cikin malaman musulunci suke fada kan hukuncin da Ibrahim Sarki Yola ya zartar.