A bangare guda suma daliban kwalejin Bethel na Kaduna 31 na hannun ‘yan bindigar Dajin, bayan sakin 47 a watan jiya, wadanda zuwa yanzu suka cika kwanaki 72 a tsare.
Matsalar garkuwa da mutane don neman fansa ta zama ruwan dare a arewacin Najeriyar inda lamarin ya fi tsananta a jihohin Kaduna, Zamfara, Neja da kuma Kebbi baya ga jihar Katsina ko da tuni mahukuntan kasar suka fara daukar matakin kawo karshen matsalar bayan luguden wutar Soji a jihar zamfara.
Wasu alkaluma sun nuna yadda ‘yan bindigar dajin suka yi garkuwa da mutane dubu 2 da 371 cikin watanni shidan farkon shekarar nan a jihohin arewa maso yammacin Najeriyar galibinsu dalibai yayinda suka hallaka wani kaso mai yawa a mabanbantan hare-hare.