Dalibai ‘Ba za mu lamunci karin kudin makaranta a jami’oi ba’.
Majalisar dattawan Najeriya ta shiga tsakanin kungiyar daliban arewacin kasar da kuma hukumomin jami’o’in yankin game da maganar karin kudin makaranta.
‘Ya’yan kungiyar daliban arewacin Najeriyar sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga game da karin kudin karatu a makarantun yankin.
Kungiyar daliban ta ce batun karin kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki zai kasance wata babbar matsala ga daliban da ma iyayensu.
Jamilu Aliyu Chiranci, shi ne shugaban gamayyar daliban arewacin Najeriya, ya ce bai kamata a kara kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki a Najeriya na matsin tattalin arziki da rashin aikin yi ga kuma rashin tsaro ba.
- ASUU: Me ya sa ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ƙi janye yajin aiki?
- ASUU: Abu hudu da majalisar wakilai ta ce ta cimma da ƙungiyar malaman jami’a ta Najeriya
- Yajin aikin ASUU: Malaman jami’a sun ce ba za su koma aiki ba sai an biya su albashinsu
Shugaban daliban arewacin Najeriyar ya ce,” Mun hango mun ga gaskiya wannan mataki sam ba dai dai bane, shi ya sa muka je muka gana da shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan, in da muka kai masa korafin mu”.
Ya ce, ”mun shaida masa wannan karin fa ba maslaha ce ga dalibai ba musamman ma na arewacin Najeriya” in ji Jamilu Aliyu Chiranci.
Shugaban daliban ya ce sanata Ahmed Lawan ya fahimcesu in da ya nuna jin dadinsa na kasancewar dalibai basu dauki doka a hannunsu ba.
Ya ce, ya musu alkawarin cewa a matsayinsu na Majalisar Dattawa, za su yi duk abin da ya kamata su yi don ganin an samu rage a kudaden makarantar ko kuma yin abin da ya dace.
Shugaban daliban arewacin Najeriyar, ya ce daga karshen ganawar an cimma matsaya a kan cewa su shugabannin kungiyar daliban za su sanar da sauran daliban ‘yan uwansu da su zauna cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sannan kuma kowa ya jira tun da mahukunta sun riga sun shiga magana, to amma idan har su mahukuntan suka gaza cika alkawuransu, to suma dalibai zasu yi watsi da matsayar da aka cimma da su in ji shugaban daliban.
A nasa bangaren shugaban kwamitin majalisar dattawan mai kula da ilimi mai zurfi a makarantun Najeriya, Sanata Ahmed Babba Kaita, ya shaida wa BBC cewa a matsayinsu na shugabanni sun ga cewa ya kamata su yi maza su tare wannan matsala.
Ya ce,” Tuni shirye-shirye sun yi nisa don tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar karatun jami’a domin warware wannan matsala ganin irin yanayin da ake ciki a kasa”.
Sanata Kaita ya ce a ranar Talata 8 ga watan Fabrairun 2022, za a zauna domin tattaunawa kan wannan matsala.
A yanzu dai daliban sun zuba ido don ganin ko mahukunta za su cika musu alkawarin da aka dauka na rage kudin makaranta.