Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da aka dakatar, Abdulrasheed Bawa, ya shiga hannun jami’an tsaro na farin kaya (DSS).
An tattaro cewa, Bawa ya isa hedikwatar DSS ne da misalin karfe 9:02 na dare bayan dakatar da shi.
Wata majiya ta ce, a halin yanzu jami’an ‘yansandan sirri na tsare da shi.
Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar wa Daily Trust isar Bawa hukumarsu amma bai yi cikakken bayani ba game da lamarin.
A wani labarin na daban jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), sun cafke wani mutum mai suna Mohammed Sani Mohammed, da ya kasance mai damfara da sunan wai shi Jami’in EFCC ne, wani lokacin kuma ye ce shi soja ne da sauran bangarorin tsaro.
A wata sanarwar da EFCC ta fitar ta ce an cafke Mohammed ne a ranar Laraba yana kan sana’arsa ta damfarar mutane da sunan zai taimaka musu wajen nema musu sauki kan kesa-kesan da suke da su a wajen hukumar.
A fadin sanarwar, dan damfarar ya fada tarkonsu ne bayan da Shalkwatar hukumar da ke Enugu ta samu rahoton sirri kan yadda yake aiwatar da aikinsa na ta’addanci.
An aike da bayanan zuwa Shalkwatar hukumar da ke Kano kuma wanda ake zargin ya shiga hannu bayan shafe makwanni ana farautarsa.
Sanarwa ta ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya karbi naira miliyan 4.6.
Kazalika za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar aka kammala gudanar da bincike.