Boko Haram Dakarun rundunar sojojin Najerita na Operation Hadin Kai sun tabbatar da sake ceto ‘yar makarantar Chibok a jihar Borno Bitrus ta tsere daga sansanin yan ta’addan tare da danta namiji yan makonni bayan ceto Mary Dauda da Hauwa Joseph.
Dakarun Operations Hadin Kai, sun tabbatar da ceto wata yar makarantar Chibok, Ruth Bitrus, wacce ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tare da danta.
Babban kwamandan Operations Hadin Kai, Manjo Janar GC Musa, ne ya bayyana hakan a sansanin sojoji na Mimalarin a yayin bikin mika kayan asibiti da hukumar ci gaban arewa maso gabas ta yi don tallafawa rundunar a ranar Laraba, 20 ga watan Yuli, Daily Trust ta rahoto.
Manjo Janar Musa ya ce: “Idan za ku tuna a wasu yan makonni da suka shige, mun ceto wasu yan matan Chibok guda biyu da yaransu, ina son sanar maku cewa mun sake ceto wata a yayin ayyukan mu.
“Ba za mu hut aba har sai Leah Shaibu da sauran yan matan Chibok sun dawo sannan sun hadu da yan uwansu. Ba za mu hut aba har sai dukkansu sun dawo cikin koshin lafiya.
An ceto Ruth Bitrus ne daga dajin Sambisa tare da danta namiji.”
A tuna cewa wasu yan kwanaki da suka gabata, sojoji sun ceto wasu yan matan Chibok biyu, Mary Dauda da Hauwa Joseph, bayan sun tsere daga sansanin Boko Haram a Gazuwa, kimanin kilomita 9 zuwa karamar hukumar Bama ta jihar Borno, BBC Hausa ta rahoto.
Yan ta’addan ISWAP sun saki sabon bidiyon yadda suka yi babbar Sallah, sun yi barazanar kai hare-hare.
A wani labarin, kungiyar ta’addanci ISWAP ta saki wani sabon bidiyo da ya nuna mambobinta na shagalin babbar Sallah Eid-el-Kabir da ta wuce kwanan nan a wurare daban-daban.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana tsammanin wuraren da yan ta’addan duka yi shagalin baya wuce gaɓar Tafkin Chadi da kuma wasu ƙauyuka da ke hannun su a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa yayin da Sallah ta gabato, ƙungiyar ta yi shirin gudanar da bikin Babbar Sallah a maɓoyar mayaƙanta kuma ta naɗa Limaman da zasu jagoranci Sallah a wurare daban-daban.
Source:hausalegitng