Bangaren yada labarai na haramin Imam Hussain (S.a) ya bada labarin cewa tuni shirye shirye sunyi nisa kama daga shirya tattakin har zuwa karbar bakin da ake sa ran zasu halarcin haramin na Imam Hussain (S.a).
Tun daga nesa zaka gane cewa lallai an fara shiri sosai da sosan garke domin tabbatar da cewa taron yaumul arba’in din ya gudana cikin nasara ba tare da kowacce irin matsala ba.
Rahotanni daga irakin suna nuna cewa bana a kwai yiwuwar a wajabta yin allurar rigakafin korona kafina a bama maziyarta damar halartar wannan babbar ibada mai dinbin falala.
Tattakin arba’in dai na zaman babban taro da aka saba gudanarwa duk shekara, inda maziyarta daga mikatoci daban daban sukan taso su tattako a kafa zuwa haraminmai alfarma domin nuna soayayya gami da girmamawa ga jikan manzon Aallah Imam Hussain (S.a) gami da neman albarka da kuma yin addu’oin neman biyan bukatu.
Taron tattakin arba’in dai wanda ake gudanarwa a karbala yana zaman taro mafi yawa da ake gudanarwa a fadin duniya a wannan zamani da muke ciki.
Duk da matsaloli da bullar annaobar korona birus ta haifar amma hakan bai hana masoya Imam Hussain (S.a) tururuwa zuwan haramin nasa a duk shekara ba.
Imam hussain (S.a) shine jikan manzon Allah (S.a) shine jikan manzon Allah na biyu kuma an kashe shi ne a dajin karbala wanda yanzu birni ne a kasar Iraki, tun wancan lokacin hijira tana 61 ake samun maziyarta daga sassan duniya daban daban suna nikar gari domin ziyartar wannan bbban Imami kuma jikan manzon Allah, ma’ana dan ‘yar manzon Allah sayyida fatima (S.a), kuma dan Imam Ali (S.).
Tattakin arbain na imam hussain (S.a) yana gamuwa da soke soke musamman daga bangaren wahabiyawa amma duk da hakan babu abinda yake karawa lamarin na tattaki sai armashi da habaka yadda kasan sanyawa shuka taki.