Da in dawo Najeriya gara in mutu a can ko in zama dan gudun hijira_Inji wani dan Najeriya dake kasar Ukraine.
Wani dan Najeriya dake kasar Ukraine ya bayyana cewa, da ya dawo Najeriya gara ya zama dan gudun hijira ko kuma ya mutu acan.
Mutumin, Nnamdi Okafor dan kimanin shekaru 32 da ya fito daga jihar Anambra ya bayyana cewa, shin matsalolin Najeriya sun canjane?
Yace dan haka bai ga dalilin dawowarsa Najeriya ba, yanzu haka yana wani garine dake kusa da iyakar kasar Ukraine, kuma idan yaga yakin ya kai can, zai fice daga kasar.
Yace kai in ma kasheshi za’a yi, hakan yafiye masa.