Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da sunan Muazu Sambo, a matsayin sabon ministan da zai naɗa daga jihar Taraba ga majalisar dattijai.
Dailytrust ta ruwaito cewa Sambo zai maye gurbin tsohon ministan samar da lantarki, Sale Mamman, wanda shugaban ya sallama daga aiki tare da tsohon ministan noma, Sabo Nanono a watan Satumba da ya gabata.
Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, shine ya karanta wasikar neman amincewa da shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zamanta na yau Talata.