Shugaban hukumar kula da gidajen yarin Jihar Nasarawa, Mista Yunusa A. Ibrahim ya shaida wa kwamishinan shari’a na jihar, Barrister Labaran Shuaibu Magaji halin da gidan yarin ke ciki na cunkoso da ake fama sakamakon jan kafa wajen gudanar da shari’a.
Ya dai bayyana hakan ne a wata ziyara da kwamishin shari’ar ya kai ofishin shugaban hukumar kula da gidajen yarin da nufin hadin kai domin gudanar da aiki tare, masamman wajen ganin an kawo karshen rage aikata laifuka a fadin jihar.
Mista Yunusa ya bayyana damuwarsa kan yadda ake jan kafa wajen gudanar da shari’ar mutanin da ake zargi da aikata laifuka a Jihar Nasarawa.
Ya ce gidajen yari da ke Jihar Nasarawa ya cika da cunkoso na mutane sakamakon rashin yi wa wadanda ake zargi shari’a da za su san matsayinsu.
Ya ce adadin mutum 1,321 ake da matsuguninsu a gidajen yarin da ke fadin jihar, da suka hada da na Lafiya, Wamba, Keffi da kuma Nasarawa. Amma yanzu akwai mutum 2,069 da yawansu ya haifar da cin koson a gidajen yarin.
A cewarsa, cikinsu masu zaman jirar shari’a sun kai 1,408, sannan kan yanke wa mutum 640 hukuncin zama a gidan yari. Ya roki Kwamishinan shari’ar da ya sanya baki ga kotun da su rika gabatar da shari’a a kan lokaci domin zai rage cin koson jama’a a gidajen yari.
kwamishinan shari’a, Barrista Magaji ya ce kuddurin gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule shi ne, samar da dauwamammiyar zaman lafiya da hukunta duk wani mai laifi ta hanyar shari’a.
Ya ce ma’aikatar shari’a ta daukarwa kanta nauyin ziyararta bangaren hukumomin da ke da alaka da shari’a, kuma wannan koken da kuka gabatar za a tabbatar an warwareshi nan ba da jimawa ba.
Source: LEADERSHIPHAUSA