An tsauraran matakan tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke zamanta a kan titin Court Road da ke Jihar Kano, yayin da aka fara sauraren karar rikicin masarautar jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ‘yansanda da jami’an hukumar DSS, sun girke motocinsu a kan hanya tare da hana zirga-zirga.
Masu ababen hawa na bin hanyar Gyadi-Gyadi ko Zoo Road domin kaucewa cunkoso.
Yajin aikin da aka yi na kwanaki biyu ne, ya hana zaman babbar kotun, kan batun dawo da Sarki Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da gwamnatin Jihar Kano daga aiwatar da dokar da ta rushe masarautun jihar.
Mai shari’a Mohammed Liman ya bayar da wannan umarni ne, bayan da Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da kara.
An shirya fara zaman kotun da misalin karfe 10 na safe, a ranar Alhamis, amma aka sauya lokaci.
A wani labarin na daban faadar shugaban kasa, ta musanta dawo da ci gaba da biyan tallafin man fetur, inda ta jaddada kudirinta na janye tallafin don alfanun kasa baki daya.
Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewar gwamnatin tarayya, ta yi hasashen kashe Naira tiriliyan 5.4 2024 wajen biyan tallafin man fetur.
Amma, cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan bayanai, Bayo Onanuga, ya bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin.
Ya ce, “An jawo hankalin fadar shugaban kasa kan takardun manufofin kasafin kudi guda biyu wanda kafafen yada labarai ke yadawa.
“Muna kira ga jama’a da kafafen yada labarai da su yi watsi da wadannan takardu guda biyu su daina tattaunawa a kansu. Babu wani daftari da gwamnati ta amince da shi.”
DUBA NAN: Masu Binciken Tsohon Gwamnan Kano Ganduje Sun Fara Zama
Ya gargadi kafafen watsa labarai da suke bin diddigin bayanai yadda suke da kaucewa yada abin da zai haifar da rudani.