CISLAC ta gudanar da taronta kan sauyin yanayi a Kano a ranar alhamis 04, ga Afrilun 2024 a dakin taro na Otel din R & K da ke kan titin Magaji Rumfa.
Makasudin taron da cibiyar ta gudanar shi ne, tantance aikace-aikace, karfi da rauni na cibiyar GGWI a Nijeriya ta fuskar gaskiya da rikon amana da yaki da cin hanci da rashawa.
Mahalarta taron da suka hada da wakilan hukumar EFCC da kungiyoyi masu zaman kansu da wakilan al’umma da na kafafan yada labarai, sun tattauna tare da yin tsokaci da fito da matsaloli don lalubo mafita da samo bakin zare kan sauyin yanayi a Nijeriya.
A nasa jawabin, wakilin hakumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ya bayyana cewa hukumar a shirye take ta hada kai da cibiyar CISLAC wajen dikile ayyukan cin hanci da rashawa a hukumomi da ma’aikatun gwamnati matsawar za a taimaka musu da samun sahihan bayanai.
DUBA NAN: Tuluka Ta Zama Firaministar Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo
Babbar jami’a mai kula da harkokin shari’a a cibiyar CISLAC, Athsheba Tagwai, ta bayyana manufofi da muradun cibiyar CISLAC na yaki da almundahana da cin hanci da rashawa da sauran aikace-aikacen cibiyar, ta kuma gode wa mahalarta taron da irin gudunmowa da shawarwari da suka bayar a yayin gudanar da taron.