Cikin kwana biyu za a iya kawo karshen yajin aiki ba sai mako biyu ba – Shugaban ASUU.
Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ya ce wa’adin mako biyu da shugaban kasar ya bayar domin kawo karshen yajin aikin ya yi yawa.
A wata hira da gidan talabijin na Channels Tv, shugaban na ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce a bangarensu na malaman jami’a, cikin kwanaki biyu za a iya warware wannan matsala.
Ya kara da cewa ”mako biyu ya yi yawa, an riga an kammala tataunawa domin cimma matsaya, kawai zuwa za ku yi ku ce mana kun amince, wannan kuma ba zai wuce kwana biyu ba”
Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce ”A kowacce shekara ‘yan Najeriya na kashe kusan biliyan 200 wajen biyan kudin makaranta a jami’o’in kasar Ghana”
”Ya kamata gwamnati ta bai wa bangare ilimi fifiko a kasar nan, saboda dukkanmu mun je makaranta” in ji Shugaban.
Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda sai dai daga.
READ MORE : Taron Astana Ya Kara Karfafa Alaka Tsakanin Tehran, Ankara Da Moscow.
baya ƙungiyar ta mayar da yajin aikin na Illa Masha Allahu.