China na shirin gudanar da atisayen soji a Taiwan
Ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce China na ƙaddamar wani atisayen soji mafi girma a cikin ruwa da sararin samaniyar Taiwan.
Ta ce jiragen sojin saman China 71, ciki har da jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa ne suka shiga yankin Taiwan.
Yankin Taiwan dai na cin gashin kansa, to sai dai China na kallonsa a matsayin wani lardinta wanda take son mayarwa cikin ƙasarta.
A ‘yan watannin baya-bayan nan dai dangantaka na ƙara yin tsami tsakanin China ta Taiwan.
Ko a watan Agustan da ya gabata ma dai China ta bayyana fushinta game da ziyarar da kakakin majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin na Taiwan, ziyara ta farko da wani babban ɗan siyasar Amurka ya taɓa kai wa yankin cikin shekara 25.
Lamarin da ya sa ta mayar da martani ta hanyar shirya gagarumin atisayen soji a yankunan ruwayen da ke gaɓar Taiwan, tare da rufe hulɗar kasuwanci da tsibirin.
Read More :
Mazauna Amurka da Kanada na bikin Kirsimeti ba lantarki, cikin bala’in sanyi.
Qassem Soleimani ya gina dakaru fiye da na Amurka!
“Qassem Soleimani; Wane ne kwamandan rundunar Quds?” A Sri Lanka.
Na Musamman: Yadda Isra’ila Ta Zargi Kan Falasdinu Daga Littafi Mai Tsarki: