Chadi ta mika shugaban kungiyar anti-Balaka a Jamhuriyar Tsakiyar Afirca ga kotun duniya.
Hukumomi a Chadi sun mika wani tsohon jagoran wata kungiyar ‘yan tawaye a jamhuriyar Tsakiyar Afirca, CAR ga kotun da ke hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC).
Maxime Jeoffroy Eli Mokom shi ne ya jagoranci wasu mayakan kungiyoyin anti-balaka kuma ana tuhumarsa da aikata laifukan yaki da na cin mutuncin bil Adama a 2013 zuwa 2014.
Kotun ta mika sammacin a kamo mutumin ne tun 2018.
Kotun ta kuma ce ana tuhumar Mista Mokom mai shekara 43 da haihuwa da kisa da tashin al’umma daga wani wuri zuwa wani wurin da karfin tsiya, baya ga azabtar da su da sassare wasu sassan jikinsu da kuma shigar da kananan yara su zama sojojinsa da ma wasu manyan laifukan.
READ MORE : Wata zakanya na mayar da kumari a gidan kula da namun dawa na Sudan.
Rikici ya barke ne a watan Maris na 2013 bayan da ‘yan tawaye Musulmi da aka fi sani da Seleka su ka gwace iko a yankin. Bayan wannan matakin ne Kirista kasar suka kafa kungiyar ‘yan tawaye ta mayakan anti-Balaka.
An kashe dubban ‘yan kasar kuma akalla mutum miliyan daya sun rasa muhallansu a cikin kasar da ke tsakiyar nahiyar Afirca tun 2013, kmar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.
Sojojin Chadi sun shiga tsakani bayan rikicin na 2013 amma sun janye bayan da aka tuhume su da daukan bangaren Musulmin kasar.