Kasar Chadi ta kori Jan Christian Gordon Kricher jakadan kasar Jamus kuma ta bukaci ya bar kasar a zuwa kwana biyu.
A wata sanarwa gwamnatin kasar ta Chadi ta bayana cewa, jakadan na Jamus baya mutunta dokokin diflomasiyya kuma yana katsalandan a harkokin cikin gidan kasar ta yankin Afirka.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, kafin wannan korar dai jakadan ya sha magana kan gwamnatin kasar inda yake nuna gwamnatin kasar taki gudanar da zabe da kuma kokarin sharewa Shugaba Mahmad Idriss Deby hanya domin neman shugabancin kasar.
Kafar sadarwa ta Press T.v kuma ta rawaito cewa, za’a kori jakadan Jamus a Chadi cikin awanni 48 sakamakon hali mara kyau da kuma rashin mutunta ayyukan diflomasiyya kamar yadda gwamnatin Chad ta sanar a ranar juma’a.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labarai na Press T.V ya rawaito labarin cewa, musulmi a Landan sun raba kayan abinci a da dai dai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.
Rahoton ya bayyana kungiyoyi musulmi na agaji suna rabon abincin a dai dai lokacin da mutane ke bukatar taimako sabili da tsadar rayuwa.
Dubunnan mutane ke bin layi a masallachin gabashi na London a yankin Tower Hamlets domin karbar taimakon abincin.
Hukumar gudanarwar masallachin tace dole ne ta kara adaadin abincin da take samarwa domin musulmi su samu suyi buda baki.
Tun dai bayan bullar cutar korona masallachin dake Tower Hamlets ya samar da wani bangare na tara abinci, anyi hakan ne a shekarar 2020 domin taimakawa wadanda suka rasa ayyukan su sakamakon kulle sa’annan a kai abinci ga tsofaffi wadanda ke killace sakamakon dalilai na lafiya.
Sufia Maryam wacce kr kula da shirin a cibiyar Maryam ta bayyana cewa, adadin wadanda ke amfana daga wanan shiri kuma suka zuwa cin abincin shan ruwan na kyauta kodayaushe yana karuwa.
“A aikin da nayi a Tower Hamlets na shekaru talatin ban taba ganin irin haka ba” Inji ta.
Alam tace a kalla kullun mutane dubu ne ke zuwa cibiyar domin buda baki