Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya tura karin tawagar jami’an’yan sanda don ceto mata da kananan yara da ‘yan bindiga suka sace kwanan nan.
A cewarsa, wasu ‘yan bindiga da suka gudu ta hanyar Kucheri-Wanzamai-Gidan Chida a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara sun yi garkuwa da mata da yara a yankin.
Leadership Hausa ta samu cewa wasu gungun ‘yan bindiga da suka tsere daga Jihar Zamfara sun yi awon gaba da dimbin jama’a daga kauyuka uku na Wanzamai, Gidan Chida da Kucheri.
Galibin wadanda aka yi garkuwa da su kananan yara ne da ke aiki a gonakinsu a kauyukansu. Wasu daga cikinsu sun fito ne daga al’ummar Yankara da ke karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina.
Leadership Hausa ta kuma samu labarin cewa kwanaki kadan kafin wannan aika-aikar da aka yi garkuwa da jama’a, wata tawagar jami’an soji ta kashe wasu ‘yan bindiga guda hudu da ake zargin ‘yan bindiga ne a wani samame da suka kai a unguwar Gidan Damo da ke karamar hukumar Tsafe.
A cewar wata majiya ta kusa da rundunar sojin, dakarun Operation Hadarin Daji sun kaddamar da hare-haren ba-zata a dajin Rugu tare da fatattakar ‘yan bindiga da dama inda suka tilasta musu barin matsuguninsu.
An ba da rahoton cewa, ‘yan bindiga da dama sun samu raunuka daban-daban.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ta bukaci mazauna jihar da su yi watsi da wannan munanan kalamai da ake yadawa a wasu sassan kafafen yada labarai.
Rundunar ‘yan sandan ta kara tabbatar wa jama’a musamman iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, cewa tana aiki tare da hadin gwiwar sojoji da ’yan banga domin ceto wadanda lamarin ya shafa tare da hada su da iyalansu.
Source:LeadershipHausa