Shugaban majalisan dattawa, Ahmad Lawan ya yi ikirarin cewa tun asali babu batun bayyana sakamakon zabe ta na’urar BVAS a cikin dokar zabe ta shekarar 2022.
Lawan ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake bayar da gudunmuwarsa kan kudirin da Sanata Ibrahim Oloriegbe, mai wakiltar mazabar Kwara ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC ya yi kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu kan kin yin amfani da bayyana sakamakon zabe ta na’urar BVAS.
Shugaban majalisar dattawan, ya ce abin da majalisar ta amince da shi ne na tattara sakamakon zabe da kuma mika shi ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
A cikin kudurin na Sanata Oloriegbe, ya bukaci majalisar dattijai ta bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki na siyasa, shugabanni da kowane dan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, su bar batun maganar bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar, bisa tanadin dokar zabe.
Sanata Sani Musa, daga Jihar Neja, ya ce tun da ‘yan Nijeriya ba su yi zabe ta hanyar bayyana sakamakon zabe ta na’ura ba, batun neman INEC ta aika da sakamakon ta hanyar lantarki bai zama dole ba, saboda dokar zabe ba ta umurci hukumar zabe ta yi hakan ba.
Sai dai mahawarar ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan majalisar bisa tsarin jam’iyyar, saboda sabanin ra’ayi da sanatocin PDP suka yi, inda suka bukaci a janye kudirin.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Chukwuka Utazi, a lokacin da yake bayar da kudirinsa, ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta bi dokar zabe kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Da yake jawabi, Sanata Uche Ekwunife, jigo a jam’iyyar PDP, mai wakiltan Anambra ta tsakiya, ya dage da cewa ya kamata INEC ta bi tsarin dokar zabe.
Sanata Biodun Olujimi, wanda shi ma dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ya yi kira da a samar da zaman lafiya, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankula ta yadda za a shawo kan lamarin ba tare da jefa kasar cikin rudani ba.
Bugu da kari, Sanata Opeyemi Bamidele na jam’iyyar APC mai mulki a lokacin da yake magana kan batun, ya bukaci INEC da ta yi abin da ya dace bisa tanadin dokar zabe, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi hakuri har INEC ta samu damar kammala aikin zabe gaba daya.
Ya kuma yi kira ga bangaren shari’a da su yi abin da ya dace, inda ya yi nuni da cewa matukar dai an yi abin da ya dace, za a shawo kan duk wata hargitsi wanda za ta wanzar da zaman lafiya.
Mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Aliyu Sabi, a nasa jawabin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bari a ci gaba da gudanar da aikin domin a karfafa dimokuradiyya.
Da yawa daga cikin ‘yan majalisar sun ba da gudunmawa, domin nuna goyon bayansu ga kudirin, wanda ya kai ga amincewa da shi, bayan da shugaban majalisar ya kada kuri’a.
A jawabinsa na rufe kudirin, Lawan ya bukaci duk wanda bai gamsu da hukuncin da INEC ta yanke ba da ya garzaya kotu, amma ka da ya kawo matsala a kasar.
Source:Leadershiphausa