A bayanin da ta fitar a yau Talata, Ƙungiyar Africa Centre for Human Rights, ta ce an gudanar da bincike mai zurfi akan tsofin shugabannin sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar da kuma takwararsa na sojin ƙasa, Tukur Yusuf Burutai ai, inda bincike ya tabbatar da cewa sun bada umurnin kisan kiyashi kan ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba, ba su gani ba.
Hukumar ta ce a watan Disamban 2015, Janar Burutai ya bada umurnin kisan kiyashi akan daruruwan musulmi yan Shi’a a garin Zaria ta jihar Kaduna, kuma cikin wadanda kisan kiyashin ya rutsa da su har da mata da kananan yara, wanda ake kira Zaria massacre.
Sannan bayanin ya ce wannan kisan kiyashin da Buratai ya bada izinin ya haifar da lalacewan tsaro, wanda ya janyo wasu ayyukan zubar da jinanen ‘yan Najeriya a garuruwa daban daban daga jami’an na soji.
Kana sanarwar wanda shugaban cibiyar Dr. Ifure Atafure ya sanya wa hannu, ta ce a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, janar Burutai ya sake bada umurnin kisan fararen hula wadanda ke zanga-zangar lumana domin kawo ƙarshen ayyukan’ yan sandan SARS, inda sojin suka yi kisan kiyashi wa a Lekki Toll Gate a Jihar Lagos.
A nasa janibin kuwa, Air Marshall Sadique Abubakar zai fuskanci shari’a ne a kotun ta ICC bayan da bincike ya tabbatar da bada umurnin kisan mata da kananan yara 17 wadanda ke yin wasa a karkashin bishiyar mangoro a kauyen Sakotoku a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno a watan Afrilun 2020.
Sannan a watan Satumba 2021 dakarun sojin sama karkashin Air Marshall Sadique sun yi ruwan bama-bamai a akan fararen hula masu yawa a kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.
Har ila yau, Dakarun sojin sama a karkashin Sadique Abubakar sun hallaka fararen hula 20 masu sana’ar kamun kifi a kusa da sansanin Kwatar Daban Masara a yankin na tafkiin Chadi a watan na Afrilun 2021.
Atafure ya ce dole ne Air Marshall Sadique ya bada bahasin kan alkaba’oin da za a iya kauce wa hakan, duk kuwa da biliyoyin kudin da aka narka domin sayen makamai da jiragen yaki.
Daga cikin ayyukan take hakkin dan Adam da ake zargin rundunar sojin sama da aikatawa a karkashin Air Marshall Sadique akwai kisan kiyashi, fyade, tsare mutane ba bisa doka ba, batar da mutane, da kuma azabtar da fararen hula.
- Source: Sahara Reporters Hausa