Hambararen shugaban kasar Burkina Faso, Rock Marc Kabore, ya bayyana karon farko tun bayan da sojoji suka kifar da mulkinsa tare da tsare shi.
Kafofin yada labarai da dama sun nuno hotunan Mista Kabore, yayin da yake ganawa da tawagar kungiyar Ecowas da kuma ta MDD a ranar Litini.
Ministar harkokin wajen kasar Ghana dake jagorantar tawagar ta ecowas, ta ce tsohon shugaban kasar ta Burkina faso ya fada musu cewa yana cikin koshin lafiya, kuma yana samun ziyara ta iyalensa da kuma likitansa.
Saidai kungiyar ta sake nanata bukatar ganin an gaggauta sakin Mista kabore.
A ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata ne sojoji masu bore suka sanar da kifar da mulkin shugaba Kabore da gwamnatinsa, kuma tun lokacin suke tsare da shi.
Kungiyar Ecowas da kuma tarayyar Afrika AU, duk sun sakatar da kasar ta Burkina faso da zama mamba sakamakon juyin mulkin sojojin.
A ranar Alhamis mai zuwa Ecowas zatayi wani taro a birnin Accra domin duba halin da ake ciki a mali, Guinea da kuma Burkina faso, kasashe uku na yammacin Afrika inda sojoji suka kwace mulki.