Da yawa-yawan yan wasa dai musamman a Afrika irin su Bukayo Suna taimakawa inda suka fito dan ganin basu manta da asalin su ba.
Sadio Mane ya taimakawa kauyansu da ya fito ta hanyar gina masallaci, asibiti da kuma kai musu turken sadarwar 5G.
Ahmed Musa ya kasance yana wannan irin taimakon musamman a azumin watan ramda ga wanda suka kasance masu karafin karfi.
BigShoe kungiyar agaji da ta yi hadin gwiwa da Saka don taimaka wa yara matalauta da ayyukan kiwon lafiya, ta sanar da daukar nauyin da Bukayo yayi a cikin wani sakon da ta wallafa a Twitter a ranar Alhamis.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Kungiyar ta bayyana cewa an yi wa yaran aikin tiyata a babban asibitin kwararru da ke Kano.
“Muna alfahari da sanar dan uwanmu na BigShoe: @BukayoSaka87.
A gabanin gasar cin kofin duniya ta 2022 kan mun rufe aikin tiyata 120 na yara a Kano, Najeriya. Babban godiya ga likitoci da tawagar Asibitin kwararru na Firimiya, ”.
A nasa jawabin, Bukayo Saka ya ce a ko da yaushe yana farin cikin taimaka wa yaran da ke fuskantar kalubale su cimma burinsu. ”
A gare ni, kowane yaro yana da dama iri ɗaya don cimma burinsu kuma idan da gaske zan iya yin wani abu don taimakawa, yana da mahimmanci a gare ni in yi hakan,” in ji shi. ”
Yana sa ni farin ciki sosai, musamman idan na ga yara suna farin ciki, iyayen suna farin ciki.”
Duk da cewa ya zabi wakilcin Ingila a kan Najeriya, dan wasan mai shekaru 19 ya amince cewa yana jin alaka da Najeriya.
Ya kuma yaba BigShoe don tabbatar da aikin da gaskiya. Na ji albarkar kasancewa a matsayin da zan iya ba da gudummawa don sauƙaƙa rayuwar yara da kyautatawa ta hanyar wannan tiyatar.”
“Har yanzu ina jin alaka da Najeriya sosai.
A gare ni, yana da matukar mahimmanci in yi amfani da iyawata don samun tasiri mai kyau a inda zan iya kuma dole ne in faɗi babban godiya ga dukan ƙungiyar BigShoe don yin hakan.
Source:Legithausa