Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta kori dalibanta 27, ta kuma dakatar da wasu takwas da ta samu da aikata magudin jarabawa.
Jami’ar ta bayyana hakan ne ranar Lahadi cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktar Sashin Jarabawa da Dauka da Adana Bayanan Dalibai (DEAR), Amina Umar Abdullahi.
Daraktar ta ce hakan ya biyo bayan zaman da majalisar malaman jami’ar ta gudanar ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2023.
Haka kuma a cewarta matakin ya yi daidai da sashi na 20.17 (Ai, iii, iv, v, vi, vii, x da na xii) na dokar jami’ar.
Har wa yau, hukumar gudanarwar Jami’ar BUK ta gargadi dalibai 22 kan aikata laifuka daban-daban.
A wani labarin na daban kuma akalla fasinjoji 17 aka kubutar a ranar Litinin bayan da wani jirgin ruwa ya kife daura da gadar ‘Third Mainland Bridge’ da ke Jihar Legas.
Jirgin na ‘yan kasuwa mallakar kamfanin Fazma ya kife ne, bayan ya taso daga tashar Ikorodu da misalin karfe 6:45 na safiyar ranar kafin ya isa zuwa yankin Ebute Ero.
A cikin sanarwar da Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar, ta fitar ta bayyana cewa, jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 7 na safiyar Litinin.
A cewar hukumar ta LASWA, an samu nasarar kubutar da daukacin fasinjojin tare da ma’aikatan jirgin.
Source:LegitHausa