Dakin kwanan dalibai dai mata na BUK samu tagomashin tsaro sosai akan na maza, sakamakon wanda suke zaune ko kwana a cikinsa, musamman ma a manyan makarantun sikandire dana gaba da ita.
Akwai dakunan kwana dabam dabam na mata a jami’ar Bayero Kano (BUK), wanda ake musu lakaqi ba da sunan wasu fiattatun mata kamar Ramat, Hasiya da sauran su.
Barayin sun shiga “Nana Hall” ne inda suka yi mumunar barna satar wayoyi da ababe masu amfani.
Wata mai amfani da kafar sadarwa ta facebook kuma daliba a jami’ar tarayya ta BUk dake Kano, SUlaiman Khairat Jaruma ta rawaito a shafinta na facebook cewa barayi sun shiga dakin kwanan dalibai.
Ta ce barayin sun shiga dakin kwanann daliban ne da daddare yayin da dalibai matan ke bacci, tunda dare yayi sosai.
Jami’ar dai ta dawo daga hutun kirsimeti da sabuwar shekara a farkon satin nan da muke ciki wanda hakan yasa akwai karancin dalibai a hostel din.
Khairat ta ci gaba da cewa “Wannan shine karo na biyar da nake zaune a Hostel da barayi ke shiga suyi sata”
Ta ci gaba da cewa : “Ni abinda ya fi bani haushi shine yadda hukumar tsaron jami’ar suka ce wai muna ina har barayin suka shiga sukai satar bamu sani ba”
“To sai dai mun godewa Allah ba rauni ba jikkata ko kuma wata barazana”
Sharhin wanda suke binta a shafinsu Kimanin mutane arba’in da doriya ne suka tofa albarkacin bakinsu kan yadda wannan al’amarin ya faru, wani Beli Abubakar Nasiru yace: “Wannan abu bai dadi ba, Allah ya kiyaye gaba, Allah ya tona musu asiri”
Kawaji kuwa cewa yace “Abun bakin ciki wallahi” Shi kuwa Ahmed Umar cewa yace “Maye alhakin jami’an tsaron jami’ar, shin mai aka dauke su suyi.”
Nana Hauwa Iye Ahmadu kuwa tace “Ni fa banga amfanin sa mata jami’an tsaro a hostel din nan ba fa, sabida basu da wani amfani, duk shekara ko kuma duk zangon karatu sai an samu wani abu makamancin haka”
An Kama wani Namiji Yayi Shigar Mata Ya Shiga Dakin Kwanan Dalibai A Jami’a
An kama wani tsoho da yayi kokarin shiga dakin kwanan dalibai mata a jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria kamar yadda wata ta wallafa a shafinta.
Salam malama yau kawai sai ga wani tsohon banza na kokarin shiga hostel dinmu (Ribadu Hall) a Samaru, wajen karfe hudu na asubh aka kamashi.