Dakarun rundunar Operation Whirl Punch sun kashe kasurgumin dan ta’addan Buharin Yadi da yaransa da dama a kan iyakar Jihar Kaduna da Katsina.
Buharin Yadi ya shafe sama da shekaru goma yana ta’addanci a Arewacin Nijeriya, inda ya jagoranci satar shanu, cinikin makamai, safarar miyagun kwayoyi, da hare-hare da dama.
Dakarun sun kai farmakin ne karkashin jagorancin Manjo Janar MLD Saraso, biyo bayan rahotannin sirri da suka samu, inda aka yi kazamin artabu wanda dakarun suka hallaka akalla ‘yan bindiga 36.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya yaba wa sojojin tare da bayar da tabbacin ci gaba da bainwa jami’an tsaro goyon baya, yayin da ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani da ba su yarda da shi ba ga hukuma.
A wani labarin na daban mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke hukunci a yau Alhamis cewa tana da hurumin sauraren ƙarar da Aminu Babba Dan Agundi ya shigar kan batun tsige Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15 da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Wannan hukuncin ya bai wa Sarki Aminu Ado damar kalubalantar halaccin tsige shi a kotu.
Wannan hukuncin ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotun jihar Kano ta bayar na sauya tsige Sarki Aminu Ado da wasu sarakuna huɗu da aka tuɓe.
Hukuncin mai shari’a Mohammed ya tabbatar da cewa shari’ar Sarki Aminu za ta iya ci gaba da gudana, wanda ke nuna dambarwar shari’a kan shugabancin masarautar Kano bai ƙare ba.
Tun da farko dai babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin wucin gadi na hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar masarautar jihar ta 2024, wanda ya kai ga tsige Sarki Aminu Ado.
DUBA NAN: Kotu Zata Cigaba Da Sauraron Karar Neman Hana Ganduje Bayyana Kansa A Shugaban Jam’iyyar APC
Duk da tsige shi da kuma naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 da Gwamna Abba Yusuf ya yi, Sarki Bayero na ci gaba da yin sha’anin mulki a matsayin Sarki, inda ya ci gaba da zama a wata ƙaramar fada da ke Nassarawa a ƙarƙashin umarnin kotu.