Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki kasar Portugal bisa gayyatar Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa Yayin ziyarar aikin, za a karrama Shugaba Buhari da lambar yabo ta ‘Great Collar of the Order of Prince Henry’.
Buhari zai gana da farai ministan kasar, Antonio Costa, shugaban majalisa Dr Augusto Santo Silva da yan Najeriya mazauna Portugal.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yau, 28 ga watan Yuni, zai bar Abuja ziyarar aiki zuwa Portugal bayan gayyatar da Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa yai masa.
Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce Shugaba Buhari zai tattauna da takwararsa na Portugal, kuma za a karrama shi da lambar yabo na kasar ta ‘Great Collar of the Order of Prince Henry.’
Ya ce ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan wasu batutuwa da ya shafi kasashen biyu kuma za a rattaba hannu kan yarjejeniya da ta shafi iyakokin kasa.
Shehu ya kara da cewa Shugaba Buhari zai ziyarci majalisar Portugal ya gana da shugabanta Dr Augusto Santo Silva da Farai Minista na Portugal, Antonio Costa.
Ya ce yayin ziyarar, Buhari zai gana da kungiyan yan kasuwan Najeriya mazauna Portugal ya kuma yi wani taron daban da shugabannin kamfanoni da wasu da ake fatan za su saka jari a Najeriya.
Buhari, a cewar sanarwar kuma zai hallarci taron United Nations Ocean Conference, wanda aka fara a Lisbon a ranar Litinin 27 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli.
Shehu ya ce shugaban kasar zai tattauna da yan Najeriya mazauna Portugal a kan abubuwan da ke damunsu da cigaba a gida Najeriya, ya kara da cewa zai dawo Abuja a ranar Asabar 2 ga watan Yuli.
Wadanda za su yi wa Buhari rakiya Wadanda za su raka Buhari a tafiyar sun hada da Ministan Harkokin Cikin Gida, Geoffrey Onyeama; Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed; Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Saka Hannun Jari, Adeniyi Adebayo; Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Isa Pantami.
Saura sun hada da NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); Direkta Janar na NIA, Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar da Shugaban NiDCOM Honorable Abike Dabiri-Erewa. Dangi da ‘yan uwa na saka ‘yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari.
A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.
A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin ‘Corruption Tori Season 2’ da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.
An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.