Buhari Ya Zayyana Sharuddan Da Dantakarar Shugabancin Kasa Na APC Ya Kamata Ya cika.
Rahotanni sun bayyan cewa shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari ya bukaci dukkan gwamnonin jami’iyar ta APC da su zabi dan takarar da ya cancanta da zai kare martabar jam’iyar a zaben fidda gwani da za’a yi na shugabancin kasar ,kuma ya kamata dan takarar ya kasance wanda zai bawa talakawa karfin guiwa cin Nasara tun kafin zabe.
A cikin wani bayani da Mai Magana da yawun shugaban Najeriya Femi Adesina ya fadi cewa shugaba buhari ya fadi hakan ne a lokacin taron da yayi da gwamnoni 22 karkashin jam’iyar ta APC dakuma shugaban jam’iyar Abdullahi Adamu.
A ranar 6 da 8 ga watan yuni ne za’a gudanar da zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC, kuma ya bukaci gwamnoni dasu samar da hadin kai na cikin gida domin ganin an samu gagarumar nasara a babban zabe mai zuwa a shekara ta 2023
Har iral yau Buhari ya yi kira ga gwammnoni da su bada himma wajen kusantao da manofofin da ake son cimmawa kusa da juna ,kuma mu mayar da hankali kan irin sauye-suyen da ake samu da alumomimu da duniya take tsammani daga garemu.