Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya damu sosai da batun tsaron rayuka da dukiyoyin mutane.
Shugaban kasar ya ce a halin yanzu an shawo kan batun tsaro a kasar kuma gargadin kawo harin ba gaskiya bane.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce ba a samun karuwar barazanar tsaro sassan kasar kuma jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa rashin tsaro na karuwa a kasar.
A cewarsa, labaran da wasu kasashen yammacin duniya ke yadawa game da batun tsaro a kasar ba gaskiya bane, Legit.ng ta rahoto.
Ya Ce “An Shawo Kan Rashin Tsaro”.
Shugaban kasar ya yi magana ne yayin bude taron kwana 3 na sadarwa da aka shirya wa jami’an hulda da jama’a na hukumar tsaro ta NSCDC a ranar Laraba a Abuja.
Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin kakakinsa Femi Adesina ya ce jami’an tsaro suna daukan matakan da ya dace kan kallubalen tsaro da ake samu a sassan kasar.
Ya ce: “Duk da cewa rashin tsaro bai tafi ba, ba ya karuwa. Galibi, an shawo kan batun rashin tsaro a kasar.
Wannan ba tare da la’akari da abin da kasashen yammacin duniya ke cewa game da yanayin tsaron ba, abin da muka san cewa ba gaskiya bane.
“Jami’an tsaron mu sun kan magance matsalar tsaro a kasar.
Ban yarda da karmar karuwar rashin tsaro ba, ba karuwa abin ke yi ba, ana magance abin kuma za a cigaba da hakan har sai an kawo karshensa.”
Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani Kwana uku bayan fitar da gargadin kai harin ta’addanci, wani sabon rahoto ya ce Amurka ta bada shawarwari ga yan Najeriya don kare kansu.
Kamar yadda PRNigeria ta rahoto, a cikin shawarar ta baya-bayan nan, Amurka ta gargadi matafiya game da ziyartar jihohi 14 cikin 36 na Najeriya.
Sun ce garkuwa da mutane, ta’addanci, yan fashin teku da tada hankali na fararen hula sunyi yawa a jihohin.
Source:legithausang