Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola Olukayode matsayin alkalin alkalan Najeriya.
Kamar yadda Buhari Sallau ya bayyana, an bashi rantsuwar ne a fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari a takaitaccen biki a Abuja.
A zantawarsa da manema labarai, Mai shari’a Ariwoola yayi kira ga ‘yan siyasa da su basu damar aikinsu yayin da zaben 2023 ke gabatowa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola Olukayode matsayin tabbata ne alkalin alkalan Najeriya.
Mai shari’a Ariwoola ya karba rantsuwar kama aiki a ranar Laraba a takaitaccen bikin da aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja kafin fara taron mako-mako na majalisar zartarwar Najeriya wanda shugaban kasan yake jagoranci.
Shagalin ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ministoci da sauran alkalan kotun koli, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
An zabi mai shari’a Ariwoola matsayin alkalin kotun koli a ranar 22 ga watan Nuwamban 2011 a zamanin mulkin shugaba Goodluck Jonathan.
A wata zantawa da manema labarai, alkalin alkalan yayin kira ga ‘yan siyasa a kasar nan da su bar fannin shari’a yayin aikinsa yayin da zaben 2023 ke gabatowa inda ya sha alwashin kawo sauye-sauye a kotun jikin.
Bayan murabus din Mai shari’a Tanko Muhammad kan batun lafiyarsa, mai shari’a Ariwoola ya karba ragamar kotun matsayin mukaddashi.
A wani labari na daban, murabus din alkalan alkalan Najeriya, Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a ranar Litinin ya biyo bayan wasu manyan fadi-tashi da aka dade ana shiryawa amma aka kaddamar da su a daren Lahadi, majiyoyi da dama da suka san kan lamarin suka tabbatar wa da Daily Trust.
Majiyoyi masu karfi sun ce akasin tunanin da ake na cewa Muhammad yayi murabus da kansa ne, tirsasa shi aka yi daga cikin manyan jami’an tsaro da jami’an gwamnati.
Bayan murabus dinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, na biyu a daraja a kotun kolin, a matsayin mukaddashi alkalin alkalan Najeriya.
Source:legithausang