A halin yanzu dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da ‘yan uwan fasinjojin da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ‘yan ta’adda suka kai wa hari a ranar 28 ga watan Maris.
Taron dai ya gudana a fadar shugaba buhari kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Idan zaku iya tunawa a ranar 28 ga Maris ‘yan bindiga sun tarwatsa hanyar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, inda suka kashe wasu tare da sace fasinjoji da dama.
Ya zuwa yanzu, kashi na biyar na wadanda abin ya shafa sun sami ‘yancinsu.
Tun bayan hawan buhari karo na biyu dai tsaro yayi karanci musamman a arewacin Najeriya dama wasu yankunan kudancin Najeriya din amma a wani yanayi na ba sabun ba wanda ba’a Saba gani daga shugaba buhari ba, wannan karaon ya nuna alamun taisayawa ga wadanda rashin tsaron ke shafa.
Ko a cikin wannan sati ma dai jami’an tsaro a birnin zariya sun afka kan wasu fararen hula yayin da suke gudanar da ibadar juyayin jikan manzon Allah, Imam Hussain (R) amma ba’a ji shugaba buhari ko wani na kusa dashi sunyi magana ba tare da cewa mutane fararen hula bakwai ne suka rasa rayukan su a wannan balahira.
Rashin tsaro ya addabi rayuwar yau da kullum a Najeriya musamman a jihohin zamfara, Katsina da kuma Maiduguri wacce ta jima da Bankwana da sanin menene zaman lafiya.
A wani labarin na daban kuma buba galadima shahararren Dan siyasar nan kuma tsohon Dan gani kashenin buhari ya kama malamin addinin musulunci dinnan bangaren shi’a watau Sheikh Ibrahim Zakzaky ziyara a gidan sa dake Abuja.
Source: Leadership