Muhammadu Buhari ya shigo garin Kano da nufin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da aka yi.
Malam Bashir Ahmad ya sanar da isowar shugaban Najeriyan da safiyar nan da kimanin karfe 11:00.
Buhari ya ziyarci Kano bayan gama ziyarar kwanaki biyu da ya yi a jihar da ke makwabtaka da ita.
Da safiyar Litinin, 30 ga watan Junairu 2023, aka tabbatar da cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya iso garin Kano domin bude ayyuka.
Mai taimakawa shugaban Najeriyan a kan harkar kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad ya tabbatar da wannan a shafinsa na Facebook dazu.
Bashir Ahmaad ya ce Muhammadu Buhari ya iso Zawachiki da ke karamar hukumar Kumbotso.
Sanarwar ta fito ne da karfe 10:40 na safiyar nan
Hadimin shugaban kasar ya ce za a kaddamar da tashar kan tudu da aka gina a Dala da kuma aikin 10MW na wuta da gwamnatin tarayya ta samar.
Kamar yadda muka ji labari, Hukumar NSIA ta kasa ta dauki wannan nauyin katafaren aiki da aka yi da zai rika samar da wuta daga hasken rana.
Za a kaddamar da ayyuka a Kano Kafin nan, Mai taimakawa shuagaban na Najeriya ya ce a ziyarar kaddamar da ayyukan, za a bude ayyukan gwamnatocin tarayya da kuma na jiha.
Ahmaad wanda daga Kano ya fito, ya ce mahaifarsa ta amfana da gwamnatin Buhari a bangarorin hanyoyi, lantarki, kimiyya da fasaha, muhalli, da tsaro.
Tuni hadimin ya fara yada bayanai a kan zuwan Mai girma shugaban kasar, ya yi masu take da ‘PMB in Kano’, ma’ana shugaba Buhari a garin Kano.
Ina labarin rashin tsaro?
A wani karin haske da ya yi, Mai ba shugaban kasar shawara ya ce duk da gwamnatin Jiha na kukan barazana, hakan ba zai hana ziyarar yau ba.
BBC Hausa ta tabbatar da rahoton isowar shugaba Buhari da tawagarsa. Manyan gwamnatin Abdullahi Ganduje sun tarbe sa yayin da aka tsauraro tsaro.
Tinubu ya yi magana kan canjin kudi Rahoto ya zo cewa Bola Tinubu ya taka rawar gani wajen ganin an tsawaita wa’adin canza kudi, wanda hakan ya jawo ya makara zuwa wajen kamfe a Edo.
‘Dan takaran na jam’iyyar APC a 2023 ya sanar da Duniya hakan da ya ziyarci Sarkin Benin.
Source:LegitHausa