Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kai ziyarar aiki kasar Portugal bisa gayyatar Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa.
Yayin ziyarar aikin, za a karrama Shugaba Buhari da lambar yabo ta ‘Great Collar of the Order of Prince Henry’ Buhari zai gana da farai ministan kasar, Antonio Costa, shugaban majalisa Dr Augusto Santo Silva da yan Najeriya mazauna Portugal.
Shugaba Muhammadu Buhari dira Lisbon, babb birbirnin kasar Portugal lafiya a ranar Talata, 28 ga Yunu, 2022. Buhari Sallau, hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan a gajeren jawabi da hotunan da ya fitar a shafinsa na Facebook.
Sabuwar gwamnati ko ta-zarce a zaben 2023? | Legit TV Hausa Yace: ”Shugaban ya isa Lisbon, Portugal don ziyara tare da halartar taron teku na majalisar dinkin duniya.”
Wadanda za su yi wa Shugaban kasa rakiya Wadanda za su raka Buhari a tafiyar sun hada da Ministan Harkokin wajen Najeriys, Geoffrey Onyeama; Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed; Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Saka Hannun Jari, Adeniyi Adebayo; Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Isa Pantami.
Saura sun hada da NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); Direkta Janar na NIA, Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar da Shugaban NiDCOM Honorable Abike Dabiri-Erewa.
A wani labarin na daban Jam’iyyar PDP ta bai wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wa’adin sa’o’i 48 da ya fayyace kalaman da aka ce shi ya yi akan dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, in ba haka ba, Jam’iyyar itama za ta fallasa shi.
Jam’iyyar PDP ta yi barazanar fadawa ‘yan Nijeriya da ma duniya baki daya wanene Obasanjo a zahiri.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin, ya bayyana cewa shi da jam’iyyar PDP suna matukar mutunta tsohon shugaban kasa.
Jibrin ya kara da cewa, furucin zai zama abin takaici matuka idan furucin da aka alakanta ga Obasanjo wanda ya karade kusan dukkan jaridun Nijeriya ya Tabbata daga bakinsa ne.
Ya bayyana kalaman Obasanjo na cewa “ya yi kuskure wajen nada Atiku abokin takararsa” abin damuwa da takaici ne matuka.