Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Kano a ranar Litinin kamar yadda aka tsara.
Gwamna Abdullahi Ganduje dai ya nemi Buhari ya dakatar da zuwansa jihar saboda wasu dalilai da abun da zuwansa ka iya haifarwa.
An tattaro cewa shugaban kasar zai je ya kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin tarayya a jihar ta arewa.
Duk da adawar da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya nuna kan haka, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iya ziyartan jihar a gobe Litinin, 30 ga watan Janairu kamar yadda aka tsara, Nigerian Tribune ta rahoto.
Bincike sun nuna cewa shugaban kasar bai girgiza da hujjar da gwamnatin Kano ta kawo ba na son a dage ziyarar da zai kai jihar.
A wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a gidan gwamnatin Kano wanda ya samu halartan malamai, yan majalisa, shugabannin siyasa da yan kasuwa, Ganduje ya bayyana shawarar da suka yanke na neman shugaban kasar ya dakatar da ziyararsa.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar ta damu matuka da mawuyacin halin da jama’a ke ciki game da sauya tsaffin kudi, rahoton The Cable.
Ya ce an yanke shawarar ne don gudun duk wasu abubuwa da ka iya kaiwa ya komo.
Hakazalika, gwamnatin jihar ta aike wasika zuwa ga shugaban kasar tana sanar da shi dalilan da yasa ziyarar da yake shirin kaiwa bai kamata ba a wannan lokaci.
A cewar wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren labaran gwamnan ya saki, masu ruwa da tsaki a jihar sun goyi bayan hukuncin shawartan shugaban kasar kan kin kawo ziyara jihar.
Buhari zai kaddamar da ayyukan gwamnatin tarayya Sai dai kuma, Nigerian Tribune ta rahoto cewa Buhari ya dage kan kai ziyara Kano kamar yadda aka tsara saboda ba kaddamar da aikin gwamnatin jihar bane kawai zai kai shi, akwai wasu ayyukan gwamnatin tarayya da zai kaddamar a yayin ziyarar.
An tattaro cewa shugaban kasar ya yanke shawarar cewa zai je sannan ya kaddamar da ayyukan gwamnatin tarayya.
Tuni tawagarsa suka isa jihar kuma har zuwa daren ranar Asabar basu samu umurnin cewa su dawo Abuja ba.
Wata majiya ta fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa: “Idan gwamnan Kano ya lura da yanayin shugaba Buhari, da zai gane cewa shi ba mutum bane mai damuwa da wani bita-da-kulli.”
A yan kwanaki da suka gabata, shugaba Buhari wanda ya ziyarci Daura a jihar Katsina ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Masari ta aiwatar.
Source:LegitHausa