Ƙungiyar dattawan Arewacin Naeriya (NEF), ta ce shugaba Muhammadu Buhari abin takaici ne ga arewa.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna ranar Asabar, mai magana da awun ƙungiyar Hakem Baba-Ahmed ya ce Buhari ya yi alkawarin tabbatar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arzikin amma ya kasa yin hakan.
Ya shawarci ƴan Arewa su zaɓi cancanta a zaɓen 2023.
“An gaya wa ’yan Arewa cewa idan Buhari ya zama shugaban ƙasa za a shawo kan matsalolinsu amma komai ya sake taɓarɓarewa a ƙarƙashin mulkina, wannan ba farfaganda ba ce; ba almara ba ce, abu ne a zahiri” in ji shi..
Ya ƙara da cewa “Akwai miliyoyin ƴan gudun hijira a yankin arewa inda Buhari ya fito sakamakon munanan ayyukan ƴan bindiga, amma gwamnati ta ƙi amincewa da hakan, wannan ba ita ce Najeriyar da muka zaɓa a ƙarƙashin Shugaba Buhari ba.