Buhari Dole Masu garkuwa da ƴan makaranta za su ɗanɗana Kuɗar su.
Muhammadu Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya baiyana cewa an ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa lallai masu garkuwa da ɗalibai da lalata makarantu za su ɗanɗana kuɗar su.
Buhari ya yi wannan gargaɗi ne a wani taron ƙara wa juna sani da Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Horon Aikin Soja ta haɗa a Abuja a yau Talata.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
Ya yi kashedi kakkausa cewa Gwamnatin Taraiya ba za ta sake lamuntar lalata harkokin ilimi da ƴan ta’adda da ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane ke yi ba.
Buhari ya kuma sanar da cewa gwamnati ta ƙara zage dantse wajen yaƙi da garkuwa da mutane da ya addabi ƙasar a ƴan kwanakin nan.
“Ba zamu lamunci garkuwa da mutane ba, musamman na yara ƴan makaranta. Za mu sa ƙafar wando ɗaya da duk ma su yi. Za su ɗanɗana kuɗar su.
“Ba za mu yadda da lalata harkokin ilimi da tattalin arziki a ƙasar nan ba,” in ji Buhari.
Shugaban ya kuma baiyana cewa ya bada umarnin a hukunci mai tsanani ga duk waɗanda a ka kama da kaifin garkuwa da mutane da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa.