Kasar Amurka ta gayyaci shugabannin nahiyar Afrika, shugaban kasa Buhari
Buhari na daya daga cikinsu Za a yi wani taron tattaunawa da shugabannin Afrika da na Amurka, ana sa ran halartar jiga-jigan duniya.
Shugaba Buhari ya samu lambar karramawa daga gwamnatin kasar Guinea Bissau a cikin makon nan.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gayyaci shugabannin kasashen Afrika 49 da kuma shugaban kungiyar hadin kan Afrika zuwa wani taron shugabannin Amurka da Afrika da za a gudanar.
Za a yi wannan gagarumin taron ne a ranakun 13 zuwa 15 ga watan Disamban 2022 a birnin Washington DC, babban birnin kasar Amurka.
Wannan batu na gayyata dai ya iso Najeriya, kuma majiya tace ta samu bayanin ne a ranar Alhamis daga cikin wata sanarwa da aka fitar, rahoton Punch.
A cewar sanarwar, Biden ya yi imani da cewa, hadin kan Amurka da shugabannin Afrika, kungiyoyin farar hula, ‘yan kasuwa, mata da matasa abu ne mai muhimmanci wajen dakile kalubale masu yawa.
Manufar yin wannan taro mai dimbin tarihi Manufar wannan taro mai dimbin tarihi dai ba komai bane face habaka siyasa, tattalin arziki, dabarun hadin kai gami da tattaunawar jama’a kan manufa iri daya don ci gaban Afrika.
Hakazalika, taron zai mai da hankali ga tattauna hanyoyin samar da abinci, inganta lafiya, yanayi da dai sauran abubuwan da ke shafar kasashen duniya, Economic Confidential ta ruwaito.
A cewar jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard, taron da za a yi zai ba da damar habaka dankon zumuncin Najeriya da Amurka tare da samar da damammaki ga kasashen.
A bangare guda, taron zai taimakawa Amurka da Amurkawa wajen jaddada zamantakewa da samun damar yin mu’amala da jama’ar Afrika.
Daga nan ta bayyana fatan shugaban kasa Muhammadu zai halarta tare da ba da gudunmawarsa da ma sauran ‘yan kasa da abin ya shafa.
Kasar Guinea Bissau Ta Karrama Buhari da Babbar Karramawar Kasa
A wani labarin kuma, an gayyaci Buhari zuwa kasar Guinea Bissau, inda aka ba shi lambar yabo da karrmawa mai girma na kasar.
Hakazalila, an kaddamar da wani titi da aka sanyawa sunan Buhari, karo na biyu kenan inda aka yi irin haka a Nijar.
Kasashen Afrika na yawan mutunta shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya.T