Budurwar da ta fada tekun legas a ranar alhamis din data gabata an bayyana sunan ta da Adetutu Adedokun, wacce ma’aikaciyar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce.
Majoiyoyi sun bayyana cewa budurwa, wadda ta gaji sahun mahaifanta, jami’ar hukumar ce masu amfani da fararen kaya wajen bayar da bayannan sirri da takile rikici.
A ‘yan watannin da suka gabata, Adedokun wacce ta wuce shekara 30, ta samu wasikar yabo daga babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS a matsayin ta na ‘Jami’ar da tai fice wajen aiki a kayan gida kamar yadda kafar Channels Tv suka Ambato.
An kuma bayar da rahoton cewa saurayin wanda aka kashe ya nemi auren ta makonnin da suka gabata.
Direban motar Haya da ta hau yace Na ji suna muhawara ita da wani wanda yakai su da cece kucen daga bisani ta fita da ga motar tare da fadawa tekun Jim kadan bayan faruwar lamarin dai, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, LRT, da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas (LASWA), da jami’an hukumar DSS, suka dauki in da al’amarin ya faru.
Ba kasafai ba dai aka fiye jin kashe kai a sanadiyyar soyayya ko akasin haka a nahiyar afrika ba.
Yawancin abubuwan da suke janyo mutane su kasahe kansu basu fiye matsaltsalo na rashi, bashi ko kuma kuma wani abun kunya da wani ko wata suka aikata ba aikata ba.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, LASEMA, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya kuma ce har yanzu jami’an na bincike dan ceto gawar ta.
Source:LEGITHAUSA