Kungiyar BRCI ta yi wani bincike kan wani yaro a garin Kalabar da ke Jihar Kuros Ribas, wanda a yanzu haka yana hannun ‘yan sanda bayan kubutar da shi daga garkamewar da aka yi masa na tsawan lokaci a wani gida.
Shugaban Kungiyar BRCI, Mista Kebe Ikpi ya yaba wa kokarin ‘yan jarida waje zakulo ire-iren wannan cin zarafin a sassan Afirka.
Hukumar Kare Hakkin Bil-adama tana nuna damuwa matuka kan yadda ake cin zarafin mata da kananan yara.
Shugaban kungiyar BRCI, ya ce wani lokacin idan ‘yan jarida suka kawo irin wannan labarin sai ka ga abin tausayi kamar ba mutum ne da iyaye suka haifa ba ake yi ma haka.
Mista Kebe Ikpi ya yi kira ga kungiyoyin addinai da na gargajiya da hukumomi kan su rika wayarwa Iyaye da jama’a da kai domin dakile irin wannan cin zarafin mutane.
A wani labarin na daban Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki jami’an kiwon lafiya sama da dubu daya aiki domin bunkasa kiwon lafiya a jihar. Gwamna Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan cikin sakon da ya aike da shi wajen taron shekara-shekara wanda kungiyar likitoci ta kasa reshen Jihar Katsina ta shirya.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Lafiya, Injiniya Yakubu Nuhu Danja, ya yi bayanin cewa a duk shekara gwamnatin jihar na daukar nauyin likitoci 78 domin karo karatu a ciki da wajen kasar nan. Kamar yadda ya ce gwamnatin jihar ta kafa hukumar kula da lafiya matakin farko da hukumar taimakekeniyar kiwon lafiya ta jiha da kuma hukumar samar da magunguna ta jiha da nufin bunkasa kiwon lafiya a jihar.
Alhaji Aminu Masari ya yaba ma kungiyar likitocin a kan gudanar da tiyata ga marasa lafiya kyauta, ya amince da bai wa kungiyar fili domin gina ma ‘ya’yanta gidaje.
Gwamnan ya ce zuwa yanzu mutane akalla 2160 ne aka tabbatar sun harbu da cutar Korona a jihar.
Ya kuma kara da cewa an samu wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa a jihar sama 1000, sama da mutum sittin kuma sun rasu sakamakon annobar. Ya ce gwamnatin jihar na yin bakin kokarinta domin ganin an magance matsalar.
Da yake jawabinsa, shugaban kungiyar likitoci ta kasa reshen Jihar Katsina, Dakta Abubakar Dahiru ya bayyana cewa kungiyar ta gudanar da aikin tiyata kyauta ga marasa lafiya akalla 40 a babban asibitin Kankiya. Ya ce kungiyar ta kuma bayar da magunguna tare da duba wasu da ke tsare gidan gyara halinka kyauta.