Jihar Gombe ta shirya karɓar baƙuncin Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, a ranar Litinin inda zai ƙaddamar da shirin samar da guraben ayyuka da janyo masu zuba jari daga waje (OTNI) tare da ƙaddamar da Cibiyar Horaswa da zaƙulo Hazikan Matasa (BPO).
Cibiyar ta BPO wacce ita ce ta farko a shiyyar Arewa Maso Gabas kuma irinta mafi girma a Nijeriya, an tsara zata samar da aƙalla guraben ayyukan yi 2,000 ga matasa masu basira da hazaƙa a Jihar Gombe bisa irin jagorancin hangen nesa na Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Yanzu da aka kafa cibiyar ta BPO a Gombe, a Cibiyar Horar da Sana’o’i ta Amina Mohammed Skills Acquisition Centre da ke Bypass daura da hanyar Gombe zuwa Biu, jihar ta shirya zama cibiyar samar da kayayyaki, ta hanyar amfani da basira da hazakar matasanta.
Cibiya irin ta OTNI, hanya ce dake kawo sauyi a harkar kasuwanci da samar da fasahar ƙere-ƙere, kuma hanya ce mafi sauri da za ta samar da ayyukan yi ga matasan Jihar Gombe dama Nijeriya baki ɗaya.
A cewar sanarwar da Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya fitar, ta hanyar shiga wannan shiri, gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta ƙara nuna aniyarta na samar da ayyukan yi masu ɗorewa da baiwa matasa damar bada gudumawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.
Misilli ya ce, “Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya yana miƙa godiya ga Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasan Kashim Shettima bisa goyon baya da jajircewansa wajen bunƙasa tattalin arzikin Jihar Gombe dama Nijeriya baki ɗaya, a daidai lokacin da yake shirin karɓar baƙuncin mataimakin shugaban ƙasan da sauran baƙi.”
Duba nan: An Haramtawa Ado Gwanja Waka
“Taron ƙaddamarwar zai gudana ne a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa dake kan hanyar Gombe zuwa Bauchi da misalin ƙarfe 9:00 na safe, wanda zai samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu daga ciki da wajen kasar nan.”