Wata mata mai juna biyu ta rasa ranta yayin da masu satar mutane suka yi yunkurin sace mijinta da wasu a jihar Borno.
Sai dai, hatsabiban basu yi nasara ba, yayin da mafarauta da ‘yan sa kai su ka dakile harin gami da damko 4 daga cikin su.
Shugaban mafarautan yankin bai yi jinkirin mika su ga DPO yankin ba, inda aka mika su rundunar’yan sandan jihar don cigaba da bincike.
Wata mata mai juna biyu, Mary Barka ta rasa ranta yayin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, dauke da bindigu kirar AK 47 suka yi dirar mikiya kauyen Pelachiroma na karamar hukumar Hawul dake jihar Borno.
Ba tare da jinkiri ba shugaban mafarauta, Muhammad Shawulu Yohanna yayi nasarar cafkesu gami da mika su ga shugaban ‘yan sandan yankin Hawul, Habila Lemaka.
Kamar yadda Yohanna, shugaban ‘yan sa kai da mafarauta ya bayyana a wata tattaunawa da menema labarai a ranar Litinin, an samu labarin yadda lamarin ya auku wasu kwanaki da suka shude, bayan wadanda ake zargin sun kai farmaki kauyen tare da yunkurin sace wadanda suke hari, amma ba su yi nasara ba.
Kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa, ya bayyana alhininsa na yadda wadanda ake zargin suka halaka wata mata mai juna biyu, Mary Barka wadanda a halin yanzu suke dandana kudarsu a hannun ‘yan sanda.
“Kauyen Pelachiroma na kamar hukumar Hawul sun samu hari daga ‘yan bindiga.
Cikin hanzari na hada tawaga zuwa kauyen a wannan daren, inda muka yi nasarar kama hudu daga cikin wadanda ake zargin da suka yi yunkurin yin garkuwa da Barka Paul Sawa, saboda, shi ( Sawa) ya basu kiwon shanunsa. ”
Cikin rashin sa’a, ‘yan bindigan sun halaka matar Sawa, Mary Barka Paul Sawa.
“Hudu daga cikin wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, yayin da aka damkosu a matsayin fulani, hakan yasa tuni na mika su ga DPO na Hawul, Habila Lemaka. ”
Ana sa ran mika wadanda ake zargin rundunar ‘yan sandan jihar Borno don cigaba da bincike gami da gurfanar da su gaban kotu.” – Cewar Yohanna.
‘Yan sanda sun kama boka kan zargin damfara A wani labari na daban, ‘yan sanda a jihar Bayelsa sun cafke wani boka da ake zargi da dmafarar kwastominsa.
Ana zarginsa da yin awon gaba da kudinsu har N1.15 biliyan bayan sun kai masa ya tsarkake musu.