Bola Tinubu; Dalilan da suka sa siyasar tsohon gwamnan Lagos ta sha bamban da ta sauran ƴan siyasa.
Da alama nasarar da tsohon gwamnan Jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu, ya samu a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sa shahararsa ta ƙara fitowa fili.
Duk da cewa nasararsa ba ta zo wa wasu ƴan Najeriya da mamaki ba, amma wasu ƴan ƙasar sun yi tsammani zai sha kaye musamman ganin yadda ake zargi wasu daga cikin shugabannin jam’iyyarsa ba su mara masa baya ba.
An daɗe ana damawa da Tinubu a fagen siyasa da mulki kuma ya shahara a ƙasar Yarabawa, har ma aka ba shi sarautar Asiwaju.
Za a iya cewa Tinubu ya soma shahara ne a siyasa a lokacin da ya bayar da gudunmawa wurin kafa Jam’iyar SDP. Bayan nan ne aka zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Yammacin Jihar Legas a 1992.
A Majalisar Dattijan Najeriya, ya samu nasarar zama shugaban kwamitin da ke kula da bankuna, kuɗi da kasafi na Majalisar Dattawa – wanda babban kwamiti ne na Majalisar Dattawan Najeriya.
Ajiya maganin wata rana
Dangane da wannan lamari, BBC ta tuntuɓi Bala Ibrahim, tsohon ma’aikacin BBC kuma mai sharhi kan harkokin siyasa inda ya ce a bayyana take cewa siyasar Tinubu ta sha bamban da siyasar sauran ƴan Najeriya.
“Siyasar Tinubu siyasa ce ta gina wasu waɗanda za a yi amfani da su a gaba saɓanin siyasar sauran iyayen gidan siyasa waɗanda suke yin amfani da waɗanda suke da amfani a lokacin da ake son amfani da su kawai,” in ji Bala Ibrahim.
Ya kuma ce “ana ganin Tinubu yakan yi ajiya ne domin ƙyanƙyasa saboda gaba kuma yanzu gaban shi ne kamar lokacin da ake ciki yanzu, ana ganin ajiyarsa ta biya masa buƙatarsa ta yanzu.
A cewarsa, ya bambanta ne da sauran masu siyasar uban-gida inda ya ce galibi shi Tinubu yakan jefa ƙwallo ne domin ya ɗauka a gaba.
“A dai wannan abin da aka yi a yanzu ana ganin ajiyar da ya yi a baya ce ta biya masa buƙatarsa ta yau, ita ta share masa hawaye ko ƙishirwarsa ta wannan lokacin a yanzu.
Bala Ibrahim ya bayyana cewa Tinubu ya sha faɗar cewa yana da burin ya zama shugaban ƙasa, wanda hakan ya sa ya rinƙa tafiya yana gini kuma ginin nan da yake yi yana ajiya ne a wasu, yana gina mutane ne waɗanda yake ganin za su yi masa amfani, in ji shi.
“A wannan gini kuma, ya yi amfani da kuɗi da abubuwan duk da yake da su, idan aka kalli ƙawancesa da gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kowa ya san wannan ƙawance ba wai soyayya ba ce ta cancanta ko kuma yana son jama’ar Jihar Kano.
“Yana son ƙuri’ar Kano ne saboda Kano ce ke da mafi yawan ƙuri’u a lokacin zaɓe, hakazalika kuma ita take da mafi yawan daliget a lokacin zaɓen fitar da ɗan takara,” in ji shi.
Ƙarƙo a siyasa
BBC ta tuntuɓi Mahmud Jega, mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya, inda ya ce a ganinsa idan aka cire Atiku Abubakar, babu ɗan siyasar da ya yi ƙarko kamar Bola Ahmed Tinubu.
“Duk yawanci waɗanda suka yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007 da yawansu an daina jin su an manta da su a sha’anin siyasa.
“Amma shi ga shi sai ƙara bunƙasa kawai yake yi, shi ya sa aka san shi fiye da duk waɗanda suka yi gwamnoni a wancan lokaci.
A cewarsa, Tinubu ya nuna ƙwazo matuƙa tun a zamanin Chief MKO Abiola, kuma tun bayan rasuwar Abiola, ba a samu wani ɗan siyasa da ya yi tasiri a kudu maso yammacin Najeriya irin Tinubu ba.
“Lokacin da ya fara siyasarsa, kusan ƙasashen Yarabawa kawai ya damu da su, ba ruwansa da ƙoƙarin neman mulkin Najeriya.
“Wato gwamnatin tarayya amma daga baya shi ya zo ya yi ruwa ya yi tsaki aka samu aka haɗa wannan jam’iyya ta APC har aka kawo Yarabawa a ciki aka samu galaba.”