Jita-jita kan matantakar mai dakin shugaba Emmanuel Macron na Faransa Birgitte, ya karade kafafen yada labaran kasar a yau laraba, wanda ke bayyana cewa Birgitte Macron tun farko an haife namiji gabanin sauya halittarta zuwa Mace, jita-jitar da ke zuwa watanni gabanin zaben kasar da Macron ke neman wa’adi na biyu.
Lauyan Birgitte, Jean Ennouchi ya shaidawa manema labarai cewa tuni mai dakin shugaban ta fara shirye-shiryen shigar da kara kan batun wanda ta bayyana a matsayin taba kimarta.
Bayanai sun ce Birgette wadda ko a bara ta fuskan
Tun farko jita-jitar ta fara tsananta ne a kafafen sada zumunta kan zargin cewa Birgitte mai shekaru 68 ta sauya halittarta ne zuwa mace gomman shekaru da suka gabata.
Jita-jitar sauyin halitta ba sabon abu ba ne tsakanin fitattun mutane musamman ‘yan siyasa amma kuma bai taba faruwa a Faransa in banda yanzu akan Birgette ba.
Kafin yanzu dai mai dakin tsohon shugaban Amurka Michelle Obama ta fuskanci makamancin wannan zargi haka zalika mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris kana Firaministar New Zealand Jacinda Arden.
A wani labarin daban masu gabatar da kara a Faransa na ci gaba da bincike kan zargin da ake yiwa wani soja da yiwa abokiyar aikin sa Fyade a fadar shugaban kasar, abinda ake ganin ka iya shafawa gwamnatin shugaba Macron kashin kaji.
Sojojin biyu dai na cikin wadanda aka tura don tabbatar da tsaro a fadar shugaban kasar a ranar, a lokacin ne kuma sojan ya hilaci abokiyar aikin sa tare da yi mata Fyaden.
Sojan da ake zargi dai ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Yulin da ya gabata, sai dai kuma an bukaci da ya rika ci gaba da amsa tambayoyin jami’an tsaro duk da cewa a baya ba’a gurfanar da shi gaban kotu a hukumance ba.
Fadar shugaban Faransa dai na kokari wajen ganin cewa abin kunya bai fita ta bangaren gwamnati ba, amma da alama hakan bata yiwuwa don kuwa ko a baya-bayan nan ma kotu ta yankewa wani dogarin Shugaba Macron Hukuncin daurin shekaru 3 sakamakon naushin wani cikin masu zanga-zanga a watan Mayun 2018.