Rundunar ‘yan sandan jihar Neja a Najeriya ta bada sanarwar ceto hakimin Wawa a karamar hukumar Borgu ta jihar daga hannun ‘yan bindiga.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Wassiu Abiodun ne ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya batun ceto basaraken daga hannun ‘yan bindiga din a garin Minna a wanna Asabar.
Mr Abiodun ya ce da misalin karfe 7 da rabi ne suka yi nasarar ceto hakimin, bayan kokarin da jakmi’an ‘yan sanda suka yi.
Gwamnan Jihar Neja dake Najeriya Sani Bello, ya amince da sabuwar dokar zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga ‘yan bindiga masu satar mutane don karbar kudin fansa, da kuma masu yi musu leken asiri.
Gwamnan ya kuma yi Alla-wadai da ayyukan rashin kishin kasa da masu taimakawa ‘yan bindiga da bayanai ke yi, wadanda ya ce sun ba da gudummawa wajen dakile kokarin da hukumomin tsaro ke yi na magance ta’addancin masu satar mutane da barayin shanu.