‘Yan bindiga a Najeriya sun tare tawagar matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda suka kwashe mutane da dama suka gudu da su cikin daji.
Wani shugaban al’umma Muhammadu Umaru ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar daga cikin wadanda aka kwashe akwai makotan sa guda 4 a cikin tawagar motoci 20 dake samun rakiyar jami’an Yan Sanda.
Umaru yace akalla matafiya 70 ke cikin tawagar daga garin Udawa, yayin da yace akwai kuma Karin wasu mutane daga wasu garuruwa dake tsakanin Udawa da Buruku.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadanda su gudu cikin daji sun kira ‘yan uwan su inda suka shaida musu abinda ya faru.
Ya zuwa wannan lokaci, rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna bata tabbatar da aukuwar lamarin ba tukuna.
A wani labarin na daban Gwamnan jihar Kaduna ta Najeriya Nasir El-Rufa’I ya hakikance cewa dole ne a kashe ‘yan bindigar da ke addabar al’umma domin kuwa bai amince da zancen yi musu afuwa ko kuma gyaran halayyarsu ba.
Gwamnan ya bayyana matsayarsa ce a yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa a jiya Talata jim kadan da kammala ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari.
EL-Rufa’I ya ziyarci shugaban kasar domin yi masa bita kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan jama’a a baya-bayan nan a Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40.
Ba a karon farko ba kenan da gwamnan ya sha bayyana cewa, bai dace a yi sulhu da wadannan mutane masu kisan jama’a ba gaira ba dalili ba.