A baya -bayan nan mahara sun tsananta kai hare -hare kan kauyuka a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na jihar, inda suka kashe jami’an tsaro 21 a hare -haren da aka kai kauyukan Dama da Gangara.
Sun kuma kashe mutane 20 tare da yin garkuwa da wasu a ƙauyen Gatawa kwanan nan.
Sakamakon hare -haren da ake kai wa al’ummomin, dan majalisar mai wakiltar Sabon Birni ta Gabas a majalisar dokokin Sakkwato, Saidu Ibrahim, ya shaida wa majiyar mu kwanan nan cewa ‘yan bindiga sun karbe ikon mazabarsa.
Isa da Sabon Birni na daga cikin kananan hukumomi 14 da aka katse hanyar sadarwar wayar salula don taimakawa ayyukan soji kan ‘yan fashi.
Mazauna karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto na rayuwa ne a cikin bakin ciki sakamakon hare-hare, da barnar da ‘yan bindiga ke yi wa kauyen da kauyukan dake makwabtaka da su.
Rahotanni sun nuna cewar, makwanni biyu da suka gabata ne ‘yan bingan suka dinga shiga kauyukan, tare da kashe akalla mutane dubu hamsin, da sace shanu.
Sakamakon wannan hare-haren dubban mata dake karamar hukumar Sabon Birni sun yi gudun hijira zuwa sakatariyar karamar hukumar, da makarantar firamari na Abdulhamid dake Sabon Birni.
Jaridar Daily Trust ta wallafa labarin dake cewa, da yawa daga cikin wadannan ‘yan Gudun hijiran sun koma Tudun Sunnah a jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, yayin da akwai wasu ‘yan gudun hijiran da yawa, da suka so tafiya kasar ta Nijar, amma baza su samu damar tafiya ba, sabo da wasu dalilai.