Binciken da wani dan jarida na kafar yada labarai ta intanet, Daily Nigeria ya gudanar a kan yadda ake samun shaidar karatun Digiri ta cuwa-cuwa cikin mako shida a wata Jami’ar Kwantano da ke kasar Benin ya tayar da kura a Nijeriya cikin wannan makon inda Ministan Ilimi ya ba da umarnin dakatar da tantance duk wata shaidar karatun Digiri daga kasashen Benin da Togo.
Wakazalika, binciken wanda ya dangana har da shiga tsarin bautar kasa (NYSC) ta amfani da shaidar karatun ba tare da wata matsala ba, ya kuma jaza wa wasu jami’o’in waje guda 18 da ke Nijeriya, inda aka dakatar da harkokinsu da bayar da shaidar karatunsu nan take.
Huhukumar, ta fitar da cikakken sunayen jami’o’in da aka haramta takardar shaidar digirinsu, inda ta wallafa sunayensu a shafinta na Intanet, da suka hada da: 1. Jami’ar Kimiyya da Gudanarwa ta Port No-bo, Jamhuriyar Benin, da sauran cibiyoyin ta da ke Nijeriya. 2. Jami’ar Bolta, da ke Ghana, da sauran cibiyoyin ta a Nijeriya. 3. Jami’ar International Unibersity, Missouri, USA, Kano da Lagos, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 4. Jami’ar Collumbus, UK, tana aiki da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 5. Tiu In-ternational Unibersity, UK, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.
Sauran su ne: 6. Jami’ar Pebbles, UK, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 7. London Edternal Studies UK, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 8. Jami’ar Pilgrims da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 9. Jami’ar Kirista ta Yammacin Afirka, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 10. Jami’ar EC-Council Unibersity, Amurka, da ke da reshe a Ikeja a Jihar Legas. 11. Kwaleji Concept (London), Ilorin, da duk wasu ci-biyoyin ta a Nijeriya.
Bugu da kari, matakin ya kuma shafi 12. Jami’ar Houdegbe ta Arewacin Amurka da ke Nijeriya. 13. Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Irish a London, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 14. Jami’ar Ilimi, Winneba, Ghana, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya. 15. Jami’ar Cape Coast, Ghana, da duk wasu ci-biyoyin ta a Nijeriya. 16. Jami’ar Gamayya ta Afrika, da ke Kwatano da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya. Sai Jami’ar Yammacin Pacific, Denber, Colorado, da ke da Cibiya a Owerri da kuma 18. Jami’ar Ebangel ta Amurka da Chudick Management Academic, da ke Legas.
Binciken da aka gudanar tun da dadewa ya sa ake ta cece-kuce a kan yadda matasan kasar nan ke tafiya Kwatano suna kammala karatun Digiri cikin dan kankanin lokaci.
Sai dai yanzu bisa wannan sanarwa, ba a san ko ma’aikatar ilimin za ta fito ta wallafa sunayen Jami’o’in da ta amince da su ba a kasashen.
Source: LEADERSHIPHAUSA