Majalisar wakilai ta nuna rashin jin dadinta kan yadda wasu mabambantar hukumomin gwamnati suka bijire wa gayyatarta a ranar Litinin, domin su amsa wasu tambayoyi game bin da haramtattun kudaden Nijeriya da aka sace aka yi waje da su wadanda aka samu nasarar dawo da su gida.
Tun da farko dai, majalisar wakilai ta gayyaci hukumomin gwamnatin tarayyar ne domin su yi bayanin haramtattun kudaden Nijeriya da aka dawo da su tun daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2020.
Wannan gayyatar dai kwamitin majalisar wakilai kan kaddarori da kudaden da aka sace na gwamnati amma aka yi nasarar dawo da su tun daga shekarar 2002 zuwa 2020 yake son jin ba’asin halin da kudaden suke ciki da yadda ake amfani da su.
A yanzu dai kwamitin ya sake tura wa da takardar sammaci ga wadannan rassa na gwamnati da suka ki amsa gayyatar da aka yi masu tun da fari. Sammacin dai yana kunshe da kudurin da dan majalisar wakilan, Ibrahim Isiaka na jam’iyyar APC daga Jihar Ogun ya gabatar domin a gudanar da bincike a zaman kwamitin ranar Litinin.
Kwamitin ya bayar da sammaci ga babban sufetan ‘yan sanda na kasa da babban mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro da gwamnan Babban Bankin Nijeriya da darakta janar na hukumar NIMASA da manajan darakta na Hukumar Zuba Jari na Nijeriya.
A lokacin da dan majalisar wakilan Ibrahim Isiaka yake gabatar da kudurin a zauren majalisar, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda wadannan jami’ai na hukumomin gwamnatin suka bijire wa kwamitin majalisar wanda a cewarsa majalisar ne ta samar da su.
“Ina son in yi rokon cewa ka da bin lamarin ya tsaya hakan nan ba tare da an gabatar da lamarin a zauren majalisar ba, ya zama wajibi mu rufe zauren majalisar ta la’akari da sashi na 88 da 89 na kundin tsarin mulki idan hukumomin gwamnati suka ki girmamamu, idan ba haka ba babu amfaninmu a nan.
“Muna warware matsaloli da dama a nan da can amma kawai su bayyana a gaban kwamitin don a sami mafita don warware matsaloli da suka taso ya gagara.
“Irin wannan abu ne suke haifar da mafi yawan matsaloli da kasar nan take fuskanta, ba mun zo nan ba ne don mu bata lokacinmu, muna da wasu abubuwa da muke yi, don ba ma son mu wulakanta aikinmu na ‘yan majalisa ne ya sanya muka kasance a wurin nan.
“Ina rokon a abi wa wadannan hukumomin gwamnatin awa 72 su bayyana a gaban kwamitin, wato zuwa ranar Alhamis.
“Idan suka gaza bayyana a gaban kwamitin, to ya tabbata a yi amfani da tanajin da kundin tsarin mulki ya tanadar a kan haka,” in ji shi.
Tun da farko dai shugaban kwamitin, dan majalisar wakilai Adeogun Adejoro na jam’iyyar APC daga Jihar Ondo ya gayyaci wadannan jami’ai su bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilan domin a saurari binciken da za a gudanar. A cewarsa, wadannan jami’ai sun ki amsa gayyata da kwamitin ya yi masu ba tare da sanar da kwamitin ba a hukumance ko kuma su aiko wakilansu.
“Ban ji dadin wannan abu da wadannan hukumomi na gwamnati suka yi ba. Ina tunanin wannan tamkar a kaikaice cin mutuncin zauren majalisar wakilai ne ba wai a matsayinsa na shugaban kwamitin ba, a kaikaice kamar ba a dauki majalisar kasa a matsayin wani bangare na gwamnati.
“A saboda haka, wannan kwamiti ya aika wa da babban gwamnan bankin Nijeriya da babban sufetan ‘yan sanda da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro da darakta janar na hukumar NIMASA da su bayyana a gaban kwamitin kafin ranar Alhamis mai zuwa.
“Idan ba haka ba, to zauren majalisar za ta tsige su a mukaman da suke kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar,” a cewarsa.
Bin Bin