Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 90 afuwa saboda murnar bikin sallah, ciki har da mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa.
Ganduje yasa an sauya wadanda aka yanke wa hukuncin kisa zuwa daurin rai-da rai saboda a gamsu da yadda halayensu ya canza.
Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa fursunonin da yayi wa afuwa kyautar shanu, raguna da shinkafa dominsu ji dadin gudanar da bikin babbar Sallah.
Fursunoni 90 sun samu afuwa daga gwamnan jiahr Kano Abdullahi Umar Ganduje ciki harda fursunoni goma sha uku 13 da aka yankewa hukuncin kisa.
Rahoton BBC News HAUSA Ganduje ya aiwatar da wannnan hukuncin ne a ranar da daukacin al’ummar Musulmi ke gudanar da bikin babban Sallah a ranar Asabar 9 ga watan Yuli 2022.
A jawabin da mai Magana da yawun gidajen yarin Najeriya reshen jihar Kano, Misbahu k Nasarawa ya fitar, yace gwamna Ganduje ya biya wa mutum 77 diyar tarar da ake bin su domin fitar dasu daga gidan yarin, kuma akwai mutane 13 da aka yanke wa hukuncin kisa a baya da aka gamsu da halayensu su, wanda yasa gwamnatin Kano ta musu afuwa.
Haka kuma wasu fursunoni 3 da aka yanke wa hukuncin kisa da gwamnan ya yi musu afuwa aka mayar da hukuncinsu daurin rai da rai.
Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa fursunonin da yayi wa afuwa kyautar shanu, raguna da shinkafa domin jin dadin gudanar da bikin babbar Sallah.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida daga Faransa ranar Sallah Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo Najeriya daga kasar Faransa.