Sojojin hadin gwiwa sun kama Beleri, kasurgumin dan bindigar Najeriya da ake nema ruwa a jallo a Najeriya.
Baleri uban gida ne ga kasurgumin dan bindiga Bello Turji, wand ya addabi al’ummar yankunan Jihar Zamfara da hare-haren ta’addanci da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa.
Baleri wanda shi ma ɗan Zamfara ne ya jima yana addabar al’ummar jihar da ma wasu yankunan Nijar, musamman jihar Maradi.
Shi ne na 40 a jerin ’yan ta’adda da hukumomin Najeriya ke nema ruwa a jallo, har ta yi alkawarin lada mai tsoka ga duk wanda ya taimaka aka kamo shi.
Sojojin na Nijar sun sanar cewa an kama Beleri ne a garin Rigar Kowa Gwani da ke yankin Gidan Rumji na jihar Maradi a kasarsu.
Rundunar sojin Nijar ta ce dakarun Runduna ta Musamman mai suna Farautar Bushiya sun yi nasarar kama Beleri ne da misalin jarfe 1 a kan iyakar kasashen biyu, a jihohin Zamfaran Najeriya da kuma Maradin Jamhuriyar Najeriya.
An kama shi ne a lokacin ya yake tsaka da ganawa da yaransaa shirinsu na kai hari a Najeriya da Nijar.
A wani labarin na daban LBisa kididdigar da shafin yanar gizo mai bayani kan hare-haren bindiga na Amurka da aka san shi da suna Gun Violence Archive ya samar, an ce, yawan harbe-harben bindiga da suka auku a shekarar 2023 ya kai a kalla 654, inda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin dubu 43, wato kwatankwacin mutuwar mutane 117 a kowace rana.
Duk da haka, sakamakon yadda jam’iyyun siyasa na kasar suke maida kudade da moriyarsu ta fannin siyasa a gaban komai, sun yi kunnen uwar shegu kan abubuwan da ke faruwa ga jama’ar kasar, inda suka gaza kai wa ga cimma matsaya daya kan kayyade yawan bindigar da ‘yan kasar ke mallaka, lamarin da har ya sa al’ummar kasar suke yin hasarar rayukansu.
DUBA NAN: Masu Binciken Tsohon Gwamnan Kano Ganduje Sun Fara Zama
A hakika, hakkin dan Adam na al’ummar kasar ba shi da muhimmanci ga ‘yan siyasar Amurka, kuma hakkin Bil Adam da suke yin shelar karewa dabara ce kawai ta samun kuri’u wajen zabe, balle ma hakkin Bil Adam na al’ummomin sauran kasashe. (Mai zane da rubutu: MINA)