Kwasotomomin bankuna a Najeriya sun roki CBN ya ci gaba da sakin tsofaffi da sabbin takardun naira.
Ta bakin kungiyarsu ta ƙasa BCAN, kwastomomin sun nemi haka ne bayan hukuncin Kotun koli jiya Laraba.
Har yanzun ‘yan Najeriya na fama da karancin takardun naira lamarin da ya gurgunta kasuwanci da rayuwar yau da kullum.
‘Yan Najeriya masu amfani da bankunan kasuwanci sun bukaci babban bankin ƙasa CBN ya sako masu tsofaffi da sabbin takardun naira domin su ci gaba da hada-hadar yau da kullum da su.
Ƙungiyar kwastomomin bankuna ta ƙasa (BCAN) ita ce ta bukaci haka daga CBN biyo bayan hukuncin da Kotun koli ta yanke ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, 2023.
Rahoton jaridar The Nation ya tattaro cewa kungiyar BCAN ta bakin shugabanta na ƙasa, Uju Ogubunka, ya ce matakin da Kotu ta ɗauka ya yi daidai duba da halin da mutane ke ciki.
Ya kuma bayyana cewa idan sabbi da tsofafin takardun N200, N500 da N1000 suka ci gaba da yawo wahalhalu zasu ragu kuma tattalin arzikin mutane zai bunƙasa.
A kalaman sa, shugaban ƙungiyar kwastomomin banki, Mista Ogubunka, ya ce: “A yanzu ya kamata CBN ya umarci bankunan kasuwanci su rika baiwa mutane tsofaffi da sababbin takardun naira lokaci zuwa lokaci domin kara yawan kuɗi a hannun al’umma.”
Wane hukunci Kotun koli ta yanke?
A jiya Laraba, Kotun Koli ta umarci babban banki da ya dakatar da shirinsa na haramta amfani da tsoffin kuɗi daga ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.
Kotun ta dauki wannan mataki ne bayan gwamnatocin jihohi uku sun kai karar gwamnatin tarayya kan sabon tsarin CBN na sauya wasu takardun naira, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Bugu da ƙari, awanni bayan wannan hukunci, Asusun ba da lamuni na duniya ya shawarci CBN ya duba yuwuwar ƙara wa’adin amfani da tsohon kuɗin saboda wahalar da yan Najeriya ke sha.
A wani labarin kuma Ma’aikata Sun Yi Barazanar Rufe Bankuna Kan Hare-Haren da Ake Kai Masu Ƙungiyar ma’aikatan bankuna, Inshora da sauran ma’aikatun kuɗi a Najeriya sun ce ba zasu ci gaba da lamurtar harin da fusatattun yan Najeriya ke kai masu ba.
Zanga-zanga ta barke a wasu sassan Najeriya sakamakon wahalar karancin takardun kuɗi, lamarin da ya kai ga kai hari bankunan kasuwanci.
Source:LegitHausa