Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya kaddamar da wani sabon shirin inganta harkar bada ilimi a cikin kasar wanda ake saran jama’ar kasar su ci moriyar sa.
Shirin bunkasa ilimin da aka yiwa lakabi da ’Niger Read‘ na samun tallafin Hukumar Cigaba ta Duniya da kuma Bankin Duniya wadanda zasu zuba kudin da ya kai Dala miliyan 140 ko kuma Cefa biliyan 75.
Gwamnatin Nijar tace shirin zai taimaka wajen inganta harkar koyarwa daga bangaren malamai da samar da makarantu ingantattu da kuma shugabancin a harkar bada ilimin baki daya, wanda ke karkashin shirin sabon shugaban kasa Bazoum na ganin ya samar da cigaba a fadin kasar.
Yayin jawabi wajen bikin shugaba Bazoum Mohammed ya bayyana harkar bada ilimi a matsayin daya daga cikin manyan kudirorin da gwamnatin sa ta saka a gaba.
Shugaban yace zasu cigaba da jajircewa wajen ganin sun cimma burin su duk da matsalolin tsaron da suke fuskanta wadda ke lakume makudan kudaden da suke samu.
A wani labarin na daban kotun hukunta Manyan Laifuffuka ta ICC ta yi watsi da bukatar tsohon kwamandan ‘yan tawayen Bosnia Ratko Mladic na neman sauya hukuncin da aka masa na daurin rai da rai sakamakon samun sa da laifuffukan yaki dangane da rawar da ya taka wajen kashe Bosniyawa Musulmi maza 8,000 a Srebrenica a shekarar 1995.
Wannan hukunci na yau ya nuna cewar Mladic zai ci gaba da zama a gidan yari har iya ransa kamar yadda hukuncin kotun na shekarar 2017 ya bayyana.
Kisan mutanen da ya faru a yankin da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya shi ne mafi muni a nahiyar Turai bayan yakin duniya na biyu.
Mladic ya ki amincewa da hukuncin kotun na shekarar 2017, abin da ya sa shi daukaka kara domin ganin alkalan kotun sun sauya hukuncin.
Tsohon kwamandan da ake yi wa lakabi da ‘Mahauchin Bosnia‘ na daga cikin wadanda ake zargi na karshe da suka gurfana a gaban kotun duniya domin amsa tambayoyi dangane da kisan kare dangin da aka yi a Bosnia.