Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ta yi watsi da rahoton da aka buga a shafukan sada zumunta kan gano wasu malaman bogi da ke aiki a jami’ar.
BUK ta bayyana labarin a matsayin mara tushe..
Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano ya ce, “Babu gaskiya a ikirarin gano irin wadannan malaman bogi da ke aiki a BUK.
“A ingantaccen tsarin koyo namu, wanda za a iya tabbatar da shi a duniya Jami’armu na kan gaba a duniya.
“Saboda haka hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero, Kano na fatan jawo hankalin jama’a cewa babu malaman bogi a ma’aikatan jami’ar ba ne.”
Farfesa Sagir, ya ce akwai bukatar mutane suke tantance sahihancin labari kafin amfani da shi.
Kazalika ya ce jami’ar za ta dauki matakin shari’a a kan masu son bata wa Jami’ar suna.
A wani labarin na daban ministan Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, sakin matar Mohammed Bazoum da dansa da sojojin juyin Mulki suka yi a Nijar wani mataki ne mai ma’ana na maido da zaman lafiya a kasar da ma yankin baki daya.
Tuggar, wanda kuma ke rike da mukamin shugaban kwamitin sulhu da tsaro, ya yabawa majalisar tsaro ta kasar da ta sake su daga kullen gida tun bayan hambarar da gwamnatin Muhammadu Bazoum.
Ya kuma sake yin kira ga gwamnatin karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani da ta gaggauta sakin Mohammed Bazoum daga hannun ta.
Tuggar ya bukace su da su kyale Bazoum ya fita zuwa wata kasa, inda ya ce, hakan, zai zama wani muhimmin mataki na samar da damar ci gaba da tattaunawa kan dage takunkumi da aka kakaba wa kasar.
Ya kara da cewa, hakan na da matukar muhimmanci ga samun walwala da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijar da ma yankin baki daya.
Source: LEADERSHIPHAUSA